Likitoci na gudanar da bincike kan wasu cututtuka sama da 1,000 da suka bulla tun daga karshen watan Janairu a kauyuka biyar na lardin Equateur na kasar Congo, inda yawan zazzabin cizon sauro ya dagula kokarin gano cutar, inda kuma jami'ai suka ce kawo yanzu ba su iya tabbatar da ainihin musabbabin cutar ba.
Shugaban kula da ayyukan gaggawa na WHO Dr. Michael Ryan ya fada a wani taron tattaunawa ta yanar gizo a ranar Juma'a cewa daya daga cikin kauyukan akwai "babban zargin wani lamari na gurbata tushin wani ruwa."
Ryan bai fayyace ko yana nufin gurbatar ruwan ya faru ne bisa kuskure ko sakaci ko kuma bisa ganganci ba. Har ila yau bai bayyana kauyen da ake zargin an gurbata ruwan ba.
Ryan ya ce "Ba za mu daina bincike ba har sai mun tabbatar da takamaiman abin da ya haddasa haka ko kuma cikakken musabbabin abin da ke faruwa a nan."
An fara gano cututtukan ne a karshen watan Janairu a kauyen Boloko bayan da yara uku suka ci jemage suka mutu cikin sa'o'i 48.
An samu labarin mutane 12 sun kamu da kuma mutuwar mutane takwas a Boloko, ba tare da samun sabbin wadanda suka kamu da cutar ba tun watan Janairu, in ji jami’ai, sun kara da cewa kusan rabin mace-mace a wurin sun faru ne cikin sa’o’i da fara bayyanar alamun cuta.
Matsalolin rashin lafiya dai ta haifar da fargaba a tsakanin mazauna garin, inda wasu daga cikin su suka ce za su tsere daga kauyukan ne domin gudun kamuwa da rashin lafiya.
Masana sun ce lungu da sako na kauyukan da lamarin ya shafa ya kawo cikas wajen isa ga marasa lafiya, kuma mutane da dama sun mutu kafin ma’aikatan lafiya su kai musu dauki.
Dandalin Mu Tattauna