Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mika Mutum 20 Da Ake Zargin ‘Yan Tawayen Hutu Ne Shiri Ne Kawai - DRC


Yan Tawayen M23 Sun Kai Mayakan FDLR Kan Iyakan Rwanda
Yan Tawayen M23 Sun Kai Mayakan FDLR Kan Iyakan Rwanda

Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun musanta a ranar Lahadi cewa an kama wasu mayaka 20 da ke da alaka da kisan kiyashi da aka yi a kasar Rwanda a yankinta, inda suka kira faifan bidiyon na mika su ga Rwanda da cewa “na karya ne.”

Sanarwar ta zo ne bayan da kungiyar ‘yan tawaye ta M23 a gabashin DRC ta fada a ranar Asabar ta kame mayaka daga dakarun neman yanci ta Rwanda FDLR, kunigyar mayakan da ‘yan kabilar Hutu suka kafa wadanda suke da hannu a kisan kiyashin da aka yi wa ‘yan kabilar Tutsi a Rwanda a shekarar 1994.

Rwanda ta dade tana nuni da kasancewar kungiyar mayaka ta FDLR a gabashin DRC.

Kungiyar M23 ta kwace yankunan gabashin DRC da ke fama da rikici, masu arzikin ma’adanai a cikin watanni nan, cikin har da manyan biranan lardunan Goma da Bukavu.

Kungiyar ta M23 ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna yadda dakarunta ke mika wasu da ake zargin mayakan FDLR 20 ga Rwanda a kan wata iyaka da ke tsakanin kasashen biyu.

“Wannan lamarin ne na bogi wanda aka shirya shi da nufin bata sunan sojojin mu,” in ji hafsan hafsoshin sojojin Congo a cikin wata sanarwa da aka fitar.

Ta kara da cewa, “Wannan wani bangare na dabarun Rwanda don ya zama hujjarta ta mamaye wasu bangarori na yankunan DRC.”

“Hukumomin kasar Rwanda wadanda suka kware wurin shirya karya da magudi, sun kama tsofaffin fursinonin FDLR, tare da sanya musu sabbin riguna soja, sannan suka mika su a matsayin mayakan FDLR da aka kama a Goma.”

Babban kwamandan DRC ya kuma zargi sojojin Rwanda da “tabbatar da hukuncin kisa ba tare da shari’a ba” kan sojoji da suka jikkata da kuma marasa lafiya a wani asibitin Goma, lamarin da ke zama laifin yaki da cin zarafin bil adama,” in sanarwar.

Rikicin da ke kara kamari a gabashin DRC ya haifar da fargabar cewa zai iya rikidewa zuwa babban yakin a yanki, wanda ya hada da kasashe Rwanda, Uganda da sauran kasashe.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG