'Yan hamayya sun ayyana cewa wa’adin shugaba Embalo ya zo karshe daga ranar 27 ga watan Fabrairun 2025 wanda ke matsayin an cika shekaru 5 da ya yi rantsuwar kama aiki yayin da shi kuwa ke cewa sai a ranar 4 ga watan Satumba ne wa’adin mulkinsa zai kammala, wato ranar da ke dai-dai da wanda kotun kolin kasar ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar 29 ga watan Disamban 2019.
A bisa umurnin shugabanin kolin CEDEAO ne tawwagar hadin gwiwa da jami’an ofishin MDD mai kula da Afirka ta yamma da yankin Sahel ta yi rangadi a Guinea Bissau daga ranar 21 zuwa 28 ga watan Fabrairun 2025, inda suka gana da farko da Shugaba Umaro Sissoko Embalo kafin daga bisani suka tattauna da ‘yan siyasa, ‘yan farar hula da jami’an gwamnati da na hukumar zabe da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da zimmar samar da maslaha a rikicin siyasar da ya barke sakamakon yadda ‘yan adawa ke ganin Shugaba Embalo na kokarin zarcewa ba bisa ka’aida ba.
Lamarin dai da ke daukan hankula a kasashen sahel.
Tawaggar a sanarwar da Ambasada Bagudu Hirse ya saka wa hannu ta kara da cewa ta bullo da wani daftarin mai kunshe da tsarin da zai ba da damar shirya zabubbuka a 2025 wanda kuma tuni ta fara gabatar da shi ga bangarorin masu ruwa da tsaki a kasar.
To amma cikin yanayin da ba shiri jami’an na CEDEAO suka fice daga kasar da sanyin safiyar Asabar 1 ga watan Maris sakamakon barazanar korar da tawwagar ke fuskanta daga shugaba Umaru Sissoco.
Da yake sharhi kan wannan al’amari, kwararre kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye ya bayyana abin a matsayin wanda ke dauke da darusa da dama ta la’akari da yadda ya wakana a wani lokacin da Nijer, Mali da Burkina Faso suka fice daga kugiyar ECOWAS.
Jami’an sun ce nan gaba ne za su gabatarwa hukumar gudanarwar kungiyar rahoto hade da shawarwarin da su ke ganin zasu taimaka a shirya zabubBuka a shekarar nan ta 2025 a Guinea Bissau tare da bai wa kowane bangare damar shiga a fafata da shi. Jami’in fafutika na kungiyar Kulawa Da Rayuwa, Hamidou Sidi Fody na gargadin cewa ya kamata CEDEAO ta dauki matakai.
Shugaban wanda ke cikin wadanda ake zargin da nuna zakewa a kungiyar CEDEAO ya shiga zagayen wasu kasashe ‘yan watannin nan da suka hada da Russia, Sudan ta Kudu, Uganda da Kenya da Hadaddiyar Daular Larabawa. Ya dai bayyana ranar 30 ga watan Nuwamban 2025 a matsayin wacce za a halarci runfunan zabe, abinda ‘yan adawa suka ce ba za ta sabu ba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna