A tsarin siyasar kasar Ghana, ana dakatar da dukkan harkokin siyasa ne a jajiberin ranar zabe, wato ranar biyar ga watan Disamban shekarar zabe, dalili kenan da manyan jami’iyyun siyasar kasar guda biyu NPP mai mulki da NDC babbar ‘yar adawa suka gudanar da tarukan yakin neman zabe na karshe.