Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Na Shirin Kulla Yarjejeniyar Saka Jari Da Ukraine

Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025
Rantsar da sabon Shugaban Amurka na 45 da 47, Donald Trump Janairun 20, 2025

Trump ya ce "Wannan babban al’amari ne kuma su ‘yan Ukraine suna bukatar haka, kana hakan zai sa mu kansance a cikin kasar," inda ya kara da cewa "Zamu maido da kudadenmu." Ya ce wannan wata jarjejeniya ce da ya kamata a kulla tun kafin ya karbi ragamar mulki.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Juma’a cewa yana sa ran Ukraine zata amince da shawarar kulla yarjejeniya da zata hada da zuba jarin Amurka a albarkatunta domin taimaka Amurka ta fanso wasu tallafin tsaronta.

Muna sa ran sanya hannu kan wata yarjejeniya, nan da dan lokaci, wadda zata bamu tabbacin maido dala bilyan 400 zuwa 500,” Trump yana fadawa manema labarai a ofishinsa na Oval a lokacin da aka tambaye shi batun yiwuwar kulla yarjejeniyar.

Trump ya ce "Wannan babban al’amari ne kuma su ‘yan Ukraine suna bukatar haka, kana hakan zai sa mu kansance a cikin kasar," inda ya kara da cewa "Zamu maido da kudadenmu." Ya ce wannan wata jarjejeniya ce da ya kamata a kulla tun kafin ya karbi ragamar mulki.

Gwamnatin Trump ta bada shawarar kulla yarjejeniyar albarkatun karkashin kasa da ba a saba gani ba, wanda bangarensa mafi girma ya maida hankali kan yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine.

Kalaman shugaban sun biyo bayan rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gabatar wa da Kyiv wata sabuwar yarjejeniyar ma'adinai da aka sake shiryawa bayan da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya yi watsi da shawarar farko.

Mai ba Amurka shawara kan tsaron kasa Mike Waltz ya yi irin wadannan kalaman da safiyar Juma'a a taron masu bin akidar siyasa ta ‘yan mazan jiya na shekara-shekara a wajen Washington.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG