Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Turai Sun Bayyana Goyon Baya Ga Ukraine Bayan Ganawar Trump Da Zelenskyy


APTOPIX Trump Zelenskyy
APTOPIX Trump Zelenskyy

Shugabanni a bangarori da dama a nahiyar Turai sun sha alawashin tsayawa tare da Ukraine bayan ganawa tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy a fadar White House ta rikide ta koma zazzafar musayar yawu a ranar Juma’a, inda Trump ya kira Zelenskyy da mara da'a.

Shugabar kula da manufofin harkokin wajen kungiyar Tarayyar, Kaja Kallas ta ce "Lallai ya tabata a fili cewa duniya mai walwala tana bukatar sabon shugaba."

Ukraine Turai ce! Kuma muna tare da ita, a cewar wani sako da Kallas ta wallafa a dandalin X.

Shima shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya fada a wani sakon X cewa Ukraine zata iya dogara da Jamus da kuma Turai, yayin da Firai ministan Spain Pedro Sanchez shima ya wallafa wani sako a dandalin sada zumunta cewa, “Ukraine, Spain zata tsaya tare da ku”.

Sakon da Firai ministan Poland Donald Tusk ya fitar a dandalin X na cewa, “Dan uwa Zelenskyy, ‘yan uwa abokai na Ukraine, ba ku kadai bane.”

Shima shugaban Faransa Emmanuel Macron ya biyo sawu, inda ya fadawa manema labarai a kasar Portugal cewa, “Rasha itace azzaluma, kana Ukraine ce ake zalunta.”

Sauran shugabannin Turai, kamar shugaban Finland, da na Holland da na Jamhuriyar Czech da kuma na Norway suma sun yi wallafe-wallafe a shafukan sada zumunta suka bayyana goyon bayan su ga Ukraine.

Sai dai ba dukkan shugabannin Turai ne suka goyi bayan Ukraine ba. Firai Ministan Hungary Viktor Orban wanda ya dade yana sukar taimakon soja da Turai ke baiwa Kyiv, ya wallafa sakon X cewa, “Shugaba Donald Trump ka yi tsayin daka don kawo zaman lafiya. Koda kuwa zai kasance mawuya ci ga fahimtar mutane da dama. Godiya garekas Shugaba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG