Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattaunawar Tsagaita Wuta Tsakanin Isra'ila Da Hamas Ta Shiga Rashin Tabbas


Palestinians Reconciliation
Palestinians Reconciliation

A jiya Asabar ne aka kawo karshen matakin farko na shrin tsagaita wutar, amma sharudan yarjejeniyar sun nuna ba za a ci gaba da fada ba yayin tattaunawar mataki na biyun ba, wanda ka iya kawo karshen yakin Gazan.

Wani babban jami'in Hamas ya bayyana cewa, ba a samu wani ci gaba ba a zagayen baya bayan nan a tattaunawar tsagaita wuta a mataki na biyu tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas da Amurka ta ayyana ‘yar ta’adda, kuma babu tabbas kan ko za a ci gaba da zama.

A jiya Asabar ne aka kawo karshen matakin farkon, amma sharudan yarjejeniyar sun nuna ba za a ci gaba da fada ba yayin tattaunawar mataki na biyun ba, wanda ka iya kawo karshen yakin Gazan, kana yasa sojojin Isra’ila su fice daga yankin sannan a sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

A cewar Isra’ila mutane 32 a cikin 59 da har yanzu ake garkuwa da su a Gaza sun mutu.

Jami’ai daga Isra’ila, Qatar, Misra da kuma Amurka sun shiga tattaunawar mataki na biyun da ake gudanarwa a birnin Alkahira. Hamas bata halarcin tattaunawar ba, amma masu shiga tsakani daga Misra da Qatar za su kare muradunta.

Basem Naim, memba ne a ofishin siyasa na Hamas, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press cewa ba a samu “ci gaba ba” kafin wakilan Isra'ila su koma gida ranar Juma'a.

Babu tabbas ko wadannan masu shiga tsakani za su koma Alkahira don ci gaba da tattaunawa kamar yadda aka zata, kuma Naim ya ce bai da masaniya kan lokacin da za a ci gaba da tattaunawar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG