Da yammacin ranar Asabar TikTok ya daina aiki a Amurka, kuma ya bace daga shagunan manhajojin Apple da Google, gabanin dokar da za ta fara aiki ranar Lahadi da ta bukaci a rufe manhajar da Amurkawa miliyan 170 ke amfani da ita.
Trump ya shaida wa gidan talabijin na NBC a wata hira cewa, "wasu karin kwanaki 90 wani abu ne da za’a iya yi, domin abu ne da ya dace."
A yau Lahadi an tsara Trump zai halarci bikin shimfida furanni a makabartar Arlington, kafin ya nufi wani gangami a dandalin Capital One Arena da ke Washington.
Ya zuwa safiyar Assabar, an sami shawo kan kashi 43% na harsunan wutar Palisades, wanda ya karu daga kashi 31% na ci gaban da aka samu a ranar Juma'a, a cewar Ma'aikatar Gandun daji da Kariyar gobara ta jihar California.
Hukuncin, wanda ya biyo bayan gargadin da gwamnatin Biden ta sha yi na cewwar manhajar ta na matukar barazana ga tsaron Amurka saboda alakarta da China, zai bada damar haramcin ya fara aiki a ranar Lahadi.
Za a rantsar da Donald Trump da zababben matamakin shugaban kasa kan mukamansu a cikin babban dakin taro na Majalisar Dokokin Amurka.
Iskar da zata fara kadawa daga daren alkhamis daga Arewacin Amurka wanda ake ayyana shi da Rockies, zata yi yankin gabas zuwa yankin kudu mai nisa har zuwa tsibirin Florida cikin ‘yan kwanaki.
Mawaka Billie Eilish, da Lady Gaga da sauransu za su hallarci taron gangamin neman agaji wa wadanda ibtila’in wutar dajin California ta shafa.
Ya na bukatar ayi gyara a kundin tsarin mulkin Amurka “domin fayyace cewa babu wani shugaban kasa da ke da kariya daga laifuffukan da ya aikata yayin da ya ke kan karagar mulki.”
Yayin da ake fatan samun sauki game da gobarar dajin da ta addabi yankin Los Angeles na jahar California kuma sai ga shi wata iska na barazanar dada dagula al'amura.
Shugaban ya bayyana cewa kusan mutum 6,000 sun riga sun yi rijista don amfana da wannan shirin, kuma har an fitar da dala miliyan 5.1. daga lalitar gwamnatin tarayya.
A bara, Amurka ta zartar da dokar da za ta tilastawa ByteDance kodai ya sayar da dandalin TikTok ko kuma ya rufe shi kan nan da 19 ga watan Janairun da muke ciki.
Domin Kari
No media source currently available