Hukuncin, wanda ya biyo bayan gargadin da gwamnatin Biden ta sha yi na cewwar manhajar ta na matukar barazana ga tsaron Amurka saboda alakarta da China, zai bada damar haramcin ya fara aiki a ranar Lahadi.
Za a rantsar da Donald Trump da zababben matamakin shugaban kasa kan mukamansu a cikin babban dakin taro na Majalisar Dokokin Amurka.
Iskar da zata fara kadawa daga daren alkhamis daga Arewacin Amurka wanda ake ayyana shi da Rockies, zata yi yankin gabas zuwa yankin kudu mai nisa har zuwa tsibirin Florida cikin ‘yan kwanaki.
Mawaka Billie Eilish, da Lady Gaga da sauransu za su hallarci taron gangamin neman agaji wa wadanda ibtila’in wutar dajin California ta shafa.
Ya na bukatar ayi gyara a kundin tsarin mulkin Amurka “domin fayyace cewa babu wani shugaban kasa da ke da kariya daga laifuffukan da ya aikata yayin da ya ke kan karagar mulki.”
Yayin da ake fatan samun sauki game da gobarar dajin da ta addabi yankin Los Angeles na jahar California kuma sai ga shi wata iska na barazanar dada dagula al'amura.
Shugaban ya bayyana cewa kusan mutum 6,000 sun riga sun yi rijista don amfana da wannan shirin, kuma har an fitar da dala miliyan 5.1. daga lalitar gwamnatin tarayya.
A bara, Amurka ta zartar da dokar da za ta tilastawa ByteDance kodai ya sayar da dandalin TikTok ko kuma ya rufe shi kan nan da 19 ga watan Janairun da muke ciki.
Ma'aikatan kashe gobara a kudancin California suna ci gaba da fafatawa da gobarar daji a yankin Los Angeles, yayin da masu hasashen yanayi suka yi gargadin cewa akwai sabuwar barazanar iska mai karfi da za ta iya rura wutar gobarar.
Gobara ta mayar da unguwanni tamkar guma-gumai masu ci da wuta, inda ta hadiye gidajen attajirai da fitattun mutane da talakawa baki daya, tare da mayar da wurin kamar an yi yaki. Jami'ai sun ce akalla gine-gine 12,300 sun lalace ko konewa kurmus.
Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.
Murabus din na Smith wata alama ce ta rugujewar tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump, wadanda ke iya ƙarewa ba tare da wani sakamako na shari'a ba ga shugaban kasar mai jiran gado.
Domin Kari
No media source currently available