Dokar shugaban kasa da ta bayar da umurnin kawo karshen yancin zama dan kasa ta hanyar haihuwa a Amurka, ta haifar da muhawara a shari’ance dama a siyasance, da tambayoyi game da Dokar Tsarin Mulki ta 14th Amendment, da kuma iya karfin da shugaban kasa ke da shi.
Sashin dokar tsarin Mulki na 14th Amendment ya tabbatar da zama dan kasa ga duk mahalukin da aka Haifa a Amurka.
A yayin da yake rattaba hannu akan dokar, shugaba Trump ya ce, kamar yadda kuka sani, kasar mu ce kadai a duniya ke da irin wannan tsarin na yancin zama dan kasa ta hanyar haihuwa. Sannan ko kusa hakan bai dace ba. To amma dai zamu gani. Mu na jin cewa muna da hujja mai karfi, kuma akwai wasu mutanen da suka so aiwatar da hakan tun a gwamman shekaru.
Kasar Amurka dai daya ce daga cikin kimanin kasashe 30 dake bada damar zama dan kasa anan take ga wadanda aka Haifa a cikin kasar, da suka hada da kasashen irin su Brazil, Mexico da Canada, da sauran wasu kasashe.
Dandalin Mu Tattauna