Gobara ta mayar da unguwanni tamkar guma-gumai masu ci da wuta, inda ta hadiye gidajen attajirai da fitattun mutane da talakawa baki daya, tare da mayar da wurin kamar an yi yaki. Jami'ai sun ce akalla gine-gine 12,300 sun lalace ko konewa kurmus.
Sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa ya ce yana fatan ganin wata sabuwar alakar dangantaka da Lebanon, kwanaki bayan kasar Lebanon mai fama da rikici ta zabi shugaban kasa a wannan makon, bayan shafe shekaru biyu ana takun saka.
Murabus din na Smith wata alama ce ta rugujewar tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump, wadanda ke iya ƙarewa ba tare da wani sakamako na shari'a ba ga shugaban kasar mai jiran gado.
Bayanin lambar yabon ya bayyana cewa Paparoma “haske ne na bangaskiya, fata, da kauna da ke haskakawa a fadin duniya.”
Ofishin jakadancin Amurka a Jamhuriyar Benin ya ba da sanarwar faduwar wani jirgi farar hula mai saukar ungulu, wanda rundunar sojan Amurka a nahiyar Afirka ta AFRICOM ke amfani da shi, domin ayyukan hadin gwiwa da dakarun kasar ta Benin a fannin kiwon lafiya.
Binciken ya yi kiyasin cewa tsakanin watan Oktoban 2023 zuwa Yunin 2024, an sami mutuwar Falasdinawa sama da 64,000 sakamakon tashin hankali a Gaza, wanda ke nuni da cewa ma'aikatar lafiya ta Hamas da ke yankin, ta rage a rahoton adadin da ta bayar na wadanda suka mutu da kusan kashi 41%.
"Batun da za mu yi musu shi ne cewa, matsayin Amurka a yankin na da matukar karfi a yanzu," in ji Sullivan, a yayin da ya ke amsa tambayar Muryar Amurka a wani taron tattaunawa da 'yan jarida a jiya Juma'a.
Jami'ai sun yi gargadin cewa adadin wadanda suka mutu, wanda aka sabunta shi a yammacin ranar Alhamis, na iya karuwa, idan aka sami shawo kan gobarar mai dimbin harsuna daban-daban, inda ma'aikata za su iya karade wurin da ta mamaye.
Ba zai fuskanci zaman gidan yari, tara, ko kuma gwajin halayya ba
Likitan da ke binciken dalilin mutuwar gawa ne ya sanar da haka a yammacin jiya Alhamis.
"Na koyi darasi daga abota irin ta Jimmy Carter – kuma ya koyar da ni ta wajen tsarin rayuwarsa -- cewa halin kirki ya fi duk wani matsayi ko ikon da mu ke da shi tasiri. Martaba ke sa a iya gane cewa ya kamata a dauki kowa da mutunci da kuma girmamawa
Bayan kammala taron addu’o’i a babban cocin kasar, za a mayar da gawar Carter zuwa mahaifarsa ta Plains, dan karamin garin da ya fara tare da kare rayuwarsa ta shekaru 100
Domin Kari
No media source currently available