A jiya litinin, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa kamfanin fasahar sadarwa na Microsoft na tattaunawa da nufin mallakar TikTok, a daidai lokacin da ake tababa kan makomar manhajar a kasar.
Kamfanin Tiktok na fuskantar wata dokar Amurka da ta umarce shi ya raba gari da mamallakinsa na kasar China Bytedance ko kuma a haramta shi a Amurka.
"Idan aka tambaye ni da yammacin yau Litinin ko Microsoft na tattaunawa domin mallake TikTok, zan ce eh”, kamar yadda Trump ya shaidawa manema labarai.
“Akwai dimbin riba a Tiktok, akwai katafariyar riba a Tiktok,” kamar yadda Trump ya fada a cikin jirgin saman shugaban Amurka.
Ya kara da cewa abu ne mai kyau idan aka fafata yin takarar mallake Tiktok din.
Dokar haramta dandalin musayar faya-fayen bidiyo ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairun da muke ciki bisa damuwar cewa gwamnatin China na iya amfani da shi wajen yiwa Amurka leken asiri ko kuma tayi tasiri akan ra’ayin al’ummar kasar a boye.
Sai dai Trump ya dakatar da amfani da dokar tsawon watanni 2 da rabi, inda yake neman hanyar warware takaddamar tsakaninsa da Beijing.
Dandalin Mu Tattauna