“Wadannan matakan, somin tabi ne ma kawai,” abin da Trump ya rubuta kenan a kafar sada zumunta ta Truth Social mallakarsa. Ya kara da cewa, “Ba za mu bar gwamnatin Colombia ta ki mutunta abubuwa na ka’ida, wadanda su ka rataya a wuyarta, masu nasaba da karbar masu aikata laifuka, wadanda su ka turo su kasarmu ba.”
Tun da farko a jiya Lahadin, Shugaban Colombia, Gustavo Petro, ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da jirage dauke da bakin hauren da aka taso keyarsu daga Amurka ba, har sai gwamnatin Trump ta kirkiro wani tsari na daukar bakin hauren da “mutunci.”
Petro, ya yi wannan sanarwar cikin wani sakonnin da ya kafa a dandalin X, daga cikin sakonnin da ya kafa, akwai wani faifaiyin bidiyon bakin hauren da rahotannin suka nuna an tasa keyarsu zuwa kasar Brazil,da suke tafiya zuwa inda jirgin yake daure da sarka a kafafun su da hannayen su.
“Bakon haure ba mai laifi ba ne kuma wajibi ne a mutumta su kamar yadda ya kamata a mutumta duk wani dan Adam,” inji Petro. “Shi ya sa na ce jiragen sojin Amurka dauke da bakin haure ‘yan Colombia ya koma Amurka…. Abin da nake so shine a sako bakin hauren cikin jiragen kasuwa, ba tare da an dauke kamar masu laifi ba, zamu tarbi ‘yan kasar mu.”
Bayan sanarwar Trump, cikin wata sanarwar Petro a X, ya yiwa ministan harkokin kasuwanci da kasashen wajen kasar ya lafta wa kayakin Amurka haraji da kaso 25%.
Dandalin Mu Tattauna