'Yan rajin dakile yaduwar makamai suna fatan sabbin kalaman shugaban Amurka Donald Trump na goyon bayan dakile yaduwar makaman nukiliya zai kai ga tattaunawa da Rasha da China akan rage makamai.
Tattaunawar Amurka da Rasha da China akan dakile yaduwar makaman nukiliya da cimma yarjejeniyya “abu ne mai yiwuwa”, a cewar Trump, wanda ya yi wa mahalarta taron bunkasa tattalin arzikin duniya a Davos kasar Switzerland mako daya da ya gabata jawabi.
“Ana kashe makudan kudade akan makaman nukiya, sannan sam, ba a son yin magana akan irin barnar da su ke yi don bama so mu ji,” in ji shi. Ya kara da cewa, “Abin bakin ciki ne.”
Trump ya yi nuni da yadda a wa’adin shi na farko, ya tattauna wannan batun da shugaban Rasha Vladimir Putin.
“Shugaba Putin ya so shawarar rage yawan makaman nukiliyan da ya mallaka, kana a tunani na da duk sauran kasashen duniya suma sun amince.
Dandalin Mu Tattauna