Shugaba Jimmy Carter ya mutu a ranar 29 ga watan Disamban da ya gabata yana da shekaru 100.
An fitar da gargadi a kan yanayin hunturu a biranen Washington DC, Maryland, Virginia da West Virginia inda hadarin hunturun na farko a 2025 ya zubar da dusar kankarar da tudun ta ya kai inci 10 a wasu garuruwan.
Hukumomin tsaro sun kasance cikin shirin ko ta kwana, inda suka giggitta shingen karfe a kewayen ginin majalisar.
Johnson ya samu kuri’u 218 yayin da 215 suka nuna adawa.
Matsayar da aka gabatar a ranar Talata, za ta sasanta karar da ta shafi zargin cewa kamfanin na Apple ya saita na’urar ta Siri da gangan domin ta rika nadar tattaunawar mutane ta hanyar wayoyin salula na iPhone, da sauran na'urorin da aka sanya musu ita tsawon fiye da shekaru goma.
Shugaban da mai dakinsa Jill za su taya iyalai da al’ummar garin da al’amarin ya shafa alhinin harin da aka kai ranar 1 ga watan Janairun da muke ciki tare da ganawa da jami’an da suke wurin,
Da farko za'a fara zaben sabon kakaki, inda mutumin da ke kan kujerar Mike Johnson, ke fafutukar ci gaba da zama a kanta.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya aike da sakon ta'aziyarsa ga iyalan mutanen da mummunan harin da aka kai da mota kan dandazon masu bikin shigowar sabuwar shekara ya rutsa dasu a birnin New Orleans a yau Laraba.
Zababben shugaban ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta gabanin a fayyace bayanan mutumin da ya kai harin a matsayin ba-Amurke mai suna Shamsud-Din Jabbar,
Domin Kari
No media source currently available