To sai dai suna, da shaharar Carter, sun fito fili ne a rayuwar bayan shugabancinsa, wadda ita ce mafi tsawo da wani shugaban kasa ta rayu a tarihin Amurka.
Jimmy Carter ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kai shekara 100 a duniya.
Darakta-Janar na hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce bama-baman da suka fada kan ginin suna da matukar ta da hankali, ta yadda kunnuwansa suka yi ta rugugi har ‘yan kwanaki bayan harin.
Hauhawar farashin kayan masarufi ya ragu a galibin kasashen duniya a 2024, sai dai hakan bai damu masu kada kuri’a ba
Matakin ya rage saura ‘yan tsirarrun da suka aikata munanan kashe-kashe sakamakon kiyayya ko ta’addanci ke fuskantar hukuncin kisa a matakin tarayya-hakan ma an tsawaita jan kafa karkashin mulkin Biden akan aiwatar da hukuncin.
Zababben shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da zabar Mark Burnett a matsayin manzon Amurka a Birtaniya.
Matambaya daga cikin tsoffin ‘yan tada kayar bayan da suka sami kwace iko da Damascus a ranar 8 ga watan Disamba, sun gana da tsoffin sojojin tare da ba su jerin tambayoyi da lambar rajista. An kuma ba su damar su tafi abinsu.
dokar da zata dakatar da rufe ofisoshin gwamnati wace zata bada dama a samarwa gwamnati kudaden da zata kashe na wucin gadi har zuwa watan Maris.
An kada kuri’un amincewa 366 da suka rinjayi na kin amincewa 34, inda dan majalisa guda kuma bai da kowane ra’ayi. Dukkanin kuri'u 34 da suka nuna adawa da kudirin na 'yan jam’iyyar Republican ne.
Jami'an Ukraine sun ce harin ya biyo ne bayan harin makami mai linzami da Rasha ta fara kai wa a Kyiv.
Karar wadda aka shigar a ranar 19 ga watan Maris a Kotun Gunduma ta Amurka da ke Kudancin Florida, ta zargi Stephanopoulos ABC News da yin munanan kalamai kan Trump tare da mummunar manufa da kaucewa gaskiya.
A bara Birtaniya ta bayyana cewa za ta shiga cikin wannan babbar yarjejeniyar ciniki tun bayan ficewar ta daga Tarayyar Turai.
Domin Kari
No media source currently available