Babban daraktan NYSC ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke yiwa ‘yan hidimar kasa rukunin “C” aji na 2 na shekarar 2024 jawabi a jihar Katsina.
Ya kara da cewa dakarun sun kuma kama barayin danyen man fetur 59 tare da kubutar da mutane 249 da masu garkuwa da mutane ke rike dasu.
An ajiye gawar hafsan da ya mutun a dakin ajiyar gawa yayin da wadanda suka jikkatan ke samun kulawar likitoci a asibitin sojoji Najeriya na 68 dake unguwar Yaba, ta birnin Legas.
A Asabar din da ta gabata, akalla mutane 11 ne suka mutu sa’ilin da wata tanka makare da fetur ta yi bindiga akan babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, dan takarar shugaban kasar jam’iyyar PDP a zaben 2023, yace kame da gurfanarwa maras tushe ta baya-bayan nan da aka yiwa Omoyele Sowore da Usman Yusuf su ne sabbin nau’ukan cin zarafin da ake yi wa jagororin adawa.
Ya kuma bayyana marigayin da ya zana tutar a matsayin wanda ya yi fice, inda yace kasancewar har yanzu kasar na amfani da zanen da ya yi alama ce dake nuna cewar ilahirin kasar na mutunta shi.
Yayin da masu ruwa da tsaki ke ci gaba da tuntubar juna kan shirin wannan taron, ga dukkan alamu komai ya kankama.
Ya kuma ce babu gudu ba ja da baya kan batun zanga0zangar gama-garin da aka shirya gudanarwa a ranar Talata 4 ga watan Febrairu mai kamawa, domin nuna rashin jin dadin kungiyar da sanarwar karin kudin kiran wayar da sayen data na baya-bayan nan.
Rahotanni sun bayyana cewar wasu mutane dauke da makamai da ake zargin makiyaya ne sun hallaka manoma 5 a kauyen Ajegunle Powerline dake karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo.
Jirgin saman kamfanin Max Air ya yi saukar gaggawa a filin saukar jiragen saman Malam Aminu Kano a daren Talatar da ta gabata.
Gangamin zai kasance gargadi kan hatsarin dake tattare da rashin dacewar karin akan al'umnar dake karbar mafi karancin albashi na ₦70, 000 da mummunan karin a farashin man fetur da kayan abinci da lantarki da hauhawar farashin kayan masarufi.
Domin Kari
No media source currently available