A jiya Alhamis, babban daraktan hukumar kula da matasa ‘yan bautar kasa a Najeriya (NYSC), Burgediya Janar Yusha’u Ahmad, ya sanarda cewar za’a fara biyan ‘yan hidimar kasa alawus din Naira 77, 000 daga watan febrairu mai kamawa.
Babban daraktan NYSC ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke yiwa ‘yan hidimar kasa rukunin “C” aji na 2 na shekarar 2024 jawabi a jihar Katsina.
Yusha’u Ahmad ya ba da tabbacin cewa karin wanda gwamnatin tarayyar kasar ta amince da shi sannan an sanya shi a cikin kasafin kudin 2025, zai fara aiki ne da zarar an zartar da kasafin.
“Gwamnatin tarayya ta riga ta amince da karin kudaden alawus din ku. Ba sabon labari bane cewa mun samu amincewar. Abin da kawai muke jira shine zartar da kasafin.
“Wannan watan na Janairu ya riga ya kare, amma da zarar an zartar da kasafin kudin zuwa doka, zaku fara karbar alawus din Naira 77, 000 a maimakon Naira 33, 000 da kuka saba karba”, a cewarsa.
Dandalin Mu Tattauna