Ya bukaci dukkanin masoyan Najeriya a fagen siyasa su dunkule a wuri guda a 2027 domin kayar da jam'iyyar APC, wacce ya zarga da yin wadaka da dukiyar kasa.
Obasanjo ya ce NNPC ya san cewa ba shi da karfin da zai iya gudanar da matatun man Najeriya amma duk da hakan ya yi fatali da tayin na Dangote.
A cewar shugaban kasar, ana sa ran sabon kamfanin ya fara aiki kafin karshen zango na 2 na sabuwar shekarar, kuma hadin gwiwa ne tsakanin hukumomin gwamnatin da suka hada da BOI, NCCC, NSIA da ma'aikatar kudin kasar da bangaren kamfanoni masu zaman kansu da kuma kamfanonin kasa da kasa.
Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan da kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a kan al'ummomin jihar Zamfara da Sokoto a sabuwar shekarar 2025.
Kungiyar kwadagon Najeriya (NLC) ta dage kan cewar wajibi ne gwamnatin tarayyar kasar ta janye kudurorin neman gyaran dokar haraji daga gaban majalisar dokokin kasar.
Batun samar da ‘yan sanda mallakar gwamnatocin jihohi a Najeriya na ci gaba da janyo tabka muhawara a tsakanin ‘yan kasar da yawansu ya haura sama da milyan dari biyu
Da alamar an fara adabo da tsadar mai da karancinsa a Najeriya
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta shawarci ‘yan kasar da ke shirin tafiya zuwa kasar Australia da su sani cewa akwai biranen kasar dake fama da tabarbarewar tsaro.
Shekarar 2024 ta kasance shekara mai cike da abubuwan tarihi, inda aka samu muhimman labarai da suka shafi siyasa, tattalin arziki, rikice-rikice, da al’amuran jin kai. Munyi duba kan wasu daga cikin manyan labarai da suka fi daukar hankali a shekarar 2024.
Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya dakatar da shugaban hukumar kula da malamai ta Teachers' Service Commission, da dukkan mukarrabansa daga aiki don gudanar da bincike kan zargin daukan malamai aiki da suka wuce ka'ida
Sanata Shehu Sani ya bayyana daya daga cikin hanyoyin da za’a bi wajen magance matsalar yin cushe cikin kasafin kudin da hukumomi da ma’aikatun gwamnati suka gabatar.
Domin Kari
No media source currently available