Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da shigar da daurarrun cikin tsarin kiwon lafiyar, domin basu damar cin gajiyar ingantaccen tsarin kiwon lafiya kyauta yayin da su ke tsare.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jin dadinsa akan sake bude matatar mai ta Warri da kamfanin man kasar NNPCL ya yi.
Ya kara da cewa an ware irin wannan karramawa ce ga fitattun jami’an gwamnati sannan ya zargi kungiyar da yin zagon kasa ga mutuncin rundunar sojin Najeriya.
Wannan kunshin na dala biliyan 2.25 ya samar da tallafin kudade domin agazawa kokarin gaggawar da Najeriya ke yi wajen daidaita tattalin arzikinta da kara tallafawa talakawa da sauran marasa galihu,
Matatar man fetur din Warri dake jihar Delta, daka iya tace ganga 125,000 a rana ta koma bakin aiki a halin yanzu.
Bincike ya nuna cewa asali Lakurawa mayaka ne da ke fada da zaluncin da suke ganin ana yi wa Buzaye da Fulani, wadanda suka yi suna kan dukiyar dabbobi da ke yawon kiwo a cikin dazuka, kafin daga baya su rikede su koma 'yan ta'adda.
Hakan na faruwa ne yayin da hukumomi ke kokarin shawo kan matsalar bullar sabuwar kungiyar Lakurawa.
An zargi dakarun tsaron kasar wadda ke yankin gabashin Afirka da kamawa da tsare mutane da dama ba bisa ka'ida ba, tun bayan zanga-zangar adawa da gwamnati da matasa suka yi a watannin Yuni da Yuli.
Manjo Janar Edward Buba, yace wata fashewa ce ta daban ta haddasa mace-macen da jikkatar amma ba dalilin hare-haren kai tsaye ba.
Bincike ya bayyana cewa Yakubu wanda ke sana'ar sayar da abinci, yana baiwa 'yan ta'addar Boko Haram din da aka tura jihar Taraba mafaka domin aikata ta'addanci.
Jamhuriyar Nijar ta zargi Najeriya da mambobin ECOWAS da hada baki da kasar Faransa da nufin hargitsa kasar.
Domin Kari
No media source currently available