Manoman sun zarta iyakar da dakarun suka shata musu domin yin noma da kamun kifi a yankin da ya zama mafaka ga mayakan ISWAP da abokan hamayyarsu na Boko Haram da nakiyoyin da aka birne da kuma yiyuwar kai hare-hare cikin dare
Kwamishinan 'yan sandan jihar Nasarawa , Shettima Muhammad, ya jagoranci tawagar jami'ansa zuwa wurin inda suka gano gawawwaki 7 tare da bin sawun maharan.
Ana zargin Obasa da kashe Naira biliyan 17 wajen saka wata kofar shiga harabar majalisar.
Gwamnatin Abacha ta kama Obasanjo a 1995 a bisa zargin kitsa juyin mulki. Sai dai, an saki tsohon shugaban kasar bayan mutuwar Abacha a 1998.
“A tabbata ana karbar haraji kan duk buhun abinci da za a fitar daga arewa a kuma daina kai shanu kai tsaye kudu maimakon haka a rika yankawa a na tura naman”
“Dakarun sojin saman Najeriya suna takatsantsan wajen tabbatar da ragewa barna da kiyaye abka ma fararen hula a ayyukan da suke aiwatar wa.
Bude babbar kasuwar shanu ta Birnin Gwari na cikin manyan sharuddan sulhun da aka yi da 'yan-bindiga kuma shugabannin kasuwar sun ce an cika wannan sharadi.
Gwamnatoci da kungiyoyin kula da kiwon lafiyar al’uma a jihohin Kano da Jigawa sun himmatu wajen magance matsalar karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar, wadanda yawan su ya zarce miliyan hudu a shiyyar arewa maso yamma da arewa maso gabas.
Kimanin watanni 10 kenan Sarakuna 2 ke ci gaba da ikirarin mallakar masarautar Kano, yayin da Alhaji Aminu Ado Bayero ke gudanar da harkokin fada a fadar sarki ta Nasarawa GRA, shi kuwa Sarki Muhammadu Sanusi II na yin nasa harkokin ne a fadar sarkin Kano ta cikin gari.
Jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta kama mutane 105, ciki harda ‘yan China 4, a wani ginin kasuwanci dake yankin Gudu na birnin Abuja.
Domin Kari
No media source currently available