A jiya Alhamis wata tankar fetur ta kama da wuta sa’ilin da take sauke mai a wani gidan man dake karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa, dake shiyar arewa maso yammacin Najeriya.
Ganau sun ce wutar ta kama ne bayan da wani mutum ya amsa wayar tarho a kusa da tankar, abin da ya sabbaba man mai saurin ci wuta kamawa. Nan da nan gobarar ta kone tankar da wani sashe na gidan man.
Sai dai, daukin gaggawar da jami’an kashe gobara da mutanen gari ya taimaka wajen hana gobarar bazuwa.
Hukumomi sun tabbatar da cewar babu asarar rai, amma har yanzu ba kai ga tantance girman asarar dukiyar da ak yi ba. Ana ci gaba da bincike domin tantance ainihin musabbabin tashin gobarar tare da magance hakan anan gaba.
A Asabar din da ta gabata, akalla mutane 11 ne suka mutu sa’ilin da wata tanka makare da fetur ta yi bindiga akan babbar hanyar Enugu zuwa Onitsha.
Gabanin hatsarin na Enugu, akalla mutane 86 ne suka hallaka sannan wasu 55 suka jikkata a ranar Asabar 18 ga watan Janairun da muke ciki, yayin da suke kwarfar mai daga wata tanka da ta fadi a jihar Neja
Dandalin Mu Tattauna