Kimanin watanni 10 kenan Sarakuna 2 ke ci gaba da ikirarin mallakar masarautar Kano, yayin da Alhaji Aminu Ado Bayero ke gudanar da harkokin fada a fadar sarki ta Nasarawa GRA, shi kuwa Sarki Muhammadu Sanusi II na yin nasa harkokin ne a fadar sarkin Kano ta cikin gari.
Jami’an hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa (EFCC) ta kama mutane 105, ciki harda ‘yan China 4, a wani ginin kasuwanci dake yankin Gudu na birnin Abuja.
Za a tura dala miliyan 50 daga cikin kudin da aka kwato zuwa aikin samar da lantarki a karkara ta hannun bankin duniya sannan za a tura ragowar dala miliyan 2 zuwa cibiyar bunkasa harkokin shari’a ta duniya domin fadada tsarin shari’a da yaki da cin hanci da rashawa.
Malaman sun yi zargi sabuwar Majalisar Gudanarwar Jami'ar da kaucewa bin tsari wajen nada Farfesa Aisha Sani Maikudi a matsayin shugabar Jami'ar, said ai kuma awkai amma kuma akwai wani rukunin Malaman da suka ce zargin ba shi da tushe.
"Batun cewa kungiyar tana samun tallafin kudade daga kasashen waje, gaskiya ce kuma suna da buri domin babu yadda za ayi wani bako ya shiga gari ba tare da samun wani alkhairi ba kuma duk sun na da nasaba da tattalin arziki".
Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta hada gwiwa da kasar China wajen fara kera makaman yaki na matsalolin tsaro cikin gida a maimakon a ci gaba da shigowa da su sakamakon wasu matsalolin da ake fama da su wajen sayowa daga waje
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirinta na kara kudin kiran waya da data sai dai ta baiwa al'ummar kasar tabbacin cewa ba zai kasance 100 bisa 100 ba kamar yadda kamfanonin suka nema.
Al’umar gundumar Dankurmi a Karamar Hukumar Mulkin Maru ta jihar Zamfara sun shiga firgici da damuwa akan wani harin ‘Yan bindiga da yayi sanadin mutuwar mutane goma sha bakwai tare da yin garkuwa da wasu sama da 300.
Tawagar mai karfi daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta raba kayan tallafi ga al’ummar da ambaliyar Ruwan sama ta yi wa barna a jihar Bauchi a shekarar bara.
Idan aka zartar da hukuncin, kowane daga cikin Ogunlaja da Daramola zai shafe shekaru 20 a gidan kaso ba tare da damar samun afuwa ba.
Domin Kari
No media source currently available