Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Cikakken Aminci A Sararin Samaniyar Najeriya - NCAA


ABUJA: An sake bude filin jirgin sama na kasa da kasa dake Abuja
ABUJA: An sake bude filin jirgin sama na kasa da kasa dake Abuja

Jirgin saman kamfanin Max Air ya yi saukar gaggawa a filin saukar jiragen saman Malam Aminu Kano a daren Talatar da ta gabata.

Hukumar kula da sufurin jiragen saman Najeriya (NCAA) ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewar akwai aminci a sararin samaniyar kasar duk kuwa da hatsarin da wani jirgin sama yayi a filin saukar jiragen saman kasa da kasa na Malam Aminu Kano da ke Kanon.

Mai rikon mukamain babban daraktan NCAA, Kyaftin Chris Najomo, ne ya ba da wannan tabbaci a hirar da aka yi dashi a shirin siyasar tashar talabijin ta Channels mai suna “Politics Today”.

“Akwai aminci sosai a sararin samaniyar Najeriya, ina mai baku tabbacin hakan,” kamar yadda yace a cikin shirin.

Jirgin saman kamfanin Max Air ya yi saukar gaggawa a filin saukar jiragen saman Malam Aminu Kano a daren Talatar da ta gabata.

Al’amarin ya faru ne da misalin karfe 10 da mintuna 57 na dare bayan da jirgin da ke dawowa daga Legas ya samu matsala da kafarsa ta gaba yayin sauka.

Ba’a ba da rahoton asarar rayuka ba a hatsarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG