Babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta Najeriya (NOA), Lanre Issa-Onilu, ya mika chakin naira miliyan 30 ga iyalan marigayi, Pa Taiwo Akinkumi, mutumin da ya zana tutar Najeriya, fiye da shekara guda bayan mutuwarsa.
Babban daraktan NOA ya bayyana hakan ne sa’ilin da ya kai ziyarar aiki ofishin hukumar da ke birnin badun, fadar gwamnatin jihar Oyo.
Issa-Onilu ya ziyarci gidan Pa Akinkunmi, inda ya mika kyautar gwamnatin tarayyar Najeriya ta Naira miliyan 30 ga iyalan marigayi, Pa Ainkunmi, wanda ya zana tutar kasar.
Ya kuma bayyana marigayin da ya zana tutar a matsayin wanda ya yi fice, inda yace kasancewar har yanzu kasar na amfani da zanen da ya yi alama ce dake nuna cewar ilahirin kasar na mutunta shi.
Dandalin Mu Tattauna