Amb. Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya za ta hada gwiwa da kasar China wajen fara kera makaman yaki na matsalolin tsaro cikin gida a maimakon a ci gaba da shigowa da su sakamakon wasu matsalolin da ake fama da su wajen sayowa daga waje
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da shirinta na kara kudin kiran waya da data sai dai ta baiwa al'ummar kasar tabbacin cewa ba zai kasance 100 bisa 100 ba kamar yadda kamfanonin suka nema.
Al’umar gundumar Dankurmi a Karamar Hukumar Mulkin Maru ta jihar Zamfara sun shiga firgici da damuwa akan wani harin ‘Yan bindiga da yayi sanadin mutuwar mutane goma sha bakwai tare da yin garkuwa da wasu sama da 300.
Tawagar mai karfi daga Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) ta raba kayan tallafi ga al’ummar da ambaliyar Ruwan sama ta yi wa barna a jihar Bauchi a shekarar bara.
Idan aka zartar da hukuncin, kowane daga cikin Ogunlaja da Daramola zai shafe shekaru 20 a gidan kaso ba tare da damar samun afuwa ba.
An sakaya sunayen sojojin da suka mutu har sai an sanar da iyalansu.
Cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce kasar nakan matsakaicin hatsarin yaduwar sabuwar kwayar cutar HMPV mai kama da mura.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Muhammad Dalijan, ya tabbatar da hakan sai dai ya ba da tabbacin cewa suna sanya idanu a kan lamarin.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Josephine Adeh ta ce an sami harin bam din ne da misalin karfe goma sha daya na safen ranar litinin.
Ya ce ya mika wa lauyoyinsa sunayen masu yada labaran karyar domin daukar matakin shari’a.
A wata takarda da ta fitar me dauke da sa hannun mataimakin daraktan ƙungiyar SERAP, Kolawole Oluwadre, kungiyar ta zargi bacewar wasu makudan kudade a kamfanin NNPCL da ya kai Naira Biliyan 825, da kuma Dalar Amurka Biliyan 2.5.
Domin Kari
No media source currently available