A cewar sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar, kasashen 2 sun amince su kulla kawance a fannoni masu mahimmanci domin al’ummar China da Najeriya su rika taimaka wa juna wajen samun manufa guda, inda zasu hada kai wajen bunkasa kawance a bangarori da dama ciki har da al’amuran da suka shafi hada-hadar kudi irinsu yin cinikayya da kudaden juna kai tsaye, domin karfafa kasuwanci a tsakaninsu tare da bada gudunmowa wajen kawo daidaito a fannin hada-hadar kudin duniya.
Sanarwar ta kuma kara da cewa, “kasashen 2 sun amince da yin hadin gwiwar kasa da kasa wajen musayar bayanan sirri akan laifuffukan da suka shafi kudi da zasu taimaka wajen yakar halasta kudaden haram da daukar nauyin ta’addanci tare da tallafawa Najeriya a kokarin da take yi na kiyaye tsarin kasuwanin hada-hada da musayar kudaden ketare tare da magance irin laifuffukan da ake aikatawa a cikinsu, ciki har halasta kudaden haram.”
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kai ziyarar aiki zuwa China, a bisa gayyatar takwaransa na kasar, xi jinping, sannan ya halarci taron koli kan kawancen China da kasashen nahiyar Afirka (FOCAC) dake gudana a birnin Beijing.
Dandalin Mu Tattauna