Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Lauyoyi Tayi Tayin Bada Kariya Kyauta Ga Masu Zanga-Zangar Tsadar Rayuwa


Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Kano dauke da tutocin kasar Rasha
Masu zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Kano dauke da tutocin kasar Rasha

Ana tsare da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 9 a kurkukun Kuje bayan da aka tuhumesu da laifin cin amanar kasa yayin da kotun ta ba da umarnin tsare mace daya tilo daga cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.

Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) tayi tayin bada kariya kyauta ga masu zanga-zangar kyamar tsadar rayuwa ta #endbadgovernance a ilahirin kotunan dake fadin kasar.

Shugaban NBA, Afan Osigwe, wanda ya sanar da hakan a shafin sada zumuntarsa na X a yau Laraba, ya kuma umarci rassan kungiyar dasu sanya idanu a kan yadda ake gudanar da shari’ar masu zanga-zangar a fadin Najeriya.

A cewarsa, “na umarci ilahirin rassan NBA dake Najeriya dasu sanya idanu a shari’ar masu zanga-zangar tsadar rayuwa ta #endbadgovernance.

“Haka kuma, na kaddamar da tsarin tallafawa masu zanga-zangar da basu da karfin daukar lauya da kariyar shari’a kyauta.”

“Tawagar lauyoyin NBA za ta kasance a kotuna domin cigaba da sanya idanu akan yadda shari’o’in dake gudana don a tabbatar da an kiyaye doka, tare da kare hakkokin dan adam na wadanda ake kara da kuma dabbaka adalci.”

Ana tsare da masu zanga-zangar tsadar rayuwa 9 a kurkukun Kuje bayan da aka tuhumesu da laifin cin amanar kasa yayin da kotun ta bada umarnin tsare mace daya tilo daga cikinsu a gidan gyaran hali na Suleja.

Masu zanga-zangar, tare da dubban ‘yan Najeriya ne, suka gudanar da bore a kan yunwa da tsadar rayuwa da rashin iya mulki ya haddasa a Najeriya, tun daga ranar 1 har izuwa 10 ga watan Agustan da ya gabata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG