Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC Ta Bukaci Gwamnati Ta Janye Karin Farashin Mai


Wata zanga-zangar lumana da NLC ta jagoranta a baya
Wata zanga-zangar lumana da NLC ta jagoranta a baya

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi maza-maza ta cire karin farashin da ta yi na litar mai a kasar.

An wayi gari a ranar Talata a sassan kasar da karin farashin litar mai inda ake sayar da shi naira 855, zuwa 897 daga naira 568 akan kowace lita.

Rahotanni sun ce kamfanin NNPC ne ya kara farashin.

Sai dai cikin wata takataitacciyar sanarwa da ta wallafa a shafukan sada zumunta a yammacin Talata, kungiyar ta NLC ta yi kira ga gwamnati da ta mayar da farashin yadda yake a da.

“Muna kira da a janye karin farashin mai da aka yi a sassan kasar ba da bata lokaci ba.” Sanarwar ta ce.

Karin farashin na zuwa ne yayin da ake fama da matsalar karancin mai a sassan kasar.

Kazalika karin na zuwa ne kwanaki biyu bayan da kamfanin NNPC ya yi korafin cewa ana bin sa makudan kudade da yawansa ya kai dala biliyan 6 na kudin masu shigo da mai.

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri ya nesanta gwamnatin da ba da umarnin karin “kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.”

“Muna masu Allah wadai da wannan ikirari da ba shi da tushe, wanda yunkuri ne na fusata jama’a.” Sanawar ta ce.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG