Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudaden Shiga Da Najeriya Ke Samu Sun Karu – NBS


Hukumar Kididdiga ta NBS a Najeriya (Hoto: Facebook/NBS)
Hukumar Kididdiga ta NBS a Najeriya (Hoto: Facebook/NBS)

Sai dai wannan sabuwar kiddiga da hukumar ta NBS ta fitar na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar tsadar rayuwa, lamarin da ya kai ga gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar a farkon watan Agusta.

Kudaden shiga da Najeriya ke samu na cikin gida ya karu da kashi 3.19% a zango na biyu na shekara ta 2024 in ji hukumar kididdiga ta NBS.

Wannan adadin ci gaba ne idan aka kwatanta da kashi 2.51% da aka samu a zangon biyu na shekara ta 2023, kuma ya fi kashi 2.98% da aka samu a zangon farko na 2024.

Hukumar ta NBS ta fitar da wannan sanarwa ce a ranar Litinin.

Irin rawar da kudaden shigar suka taka a zango na biyu na 2024 ya samu habaka ne daga bangaren ayyuka, wanda ya samu ci gaba da kashi 3.79% kuma ya ba da gudunmawar kashi 58.76% ga daukancin jimullar kudaden shiga da ake samu.

Bangaren noma ya karu da kashi 1.41%, daga kashi 1.50% da aka samu a zangon biyu na 2023. Ci gaban bangaren masana’antu ya kasance kashi 3.53%, ci gaba daga kashi -1.94% da aka samu a zangon biyu na 2023.

Kazalika hukumar ta NBS ta ruwaito cewa adadin man da ake tonowa ya karu zuwa ganga miliyan 1.41 a rana daga gangan 1.22 a rana da aka gani a shekarar da ta gabata.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi lale marhabin da habakar tattalin arzikin na Najeriya.

“Muna da kwarin gwiwar cewa tsare-tsaren da muke samarwa, muna fatar adadin man da ake samarwa zai kai ganga miliyan biyu a rana nan ba da jimawa ba.” In ji Tinubu.

Sai dai wannan sabuwar kiddiga da hukumar ta NBS ta fitar na zuwa ne yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsananciyar tsadar rayuwa, lamarin da ya kai ga gudanar da zanga-zanga a wasu sassan kasar a farkon watan Agusta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG