Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yancin Cin Gashin Kan Kananan Hukumomi: Matsayar Kotun Koli Kan Karar Da Gwamnatin Tarayya Ta Shigar


Kotun Kolin Najeriya
Kotun Kolin Najeriya

Kotun Kolin Najeriya ta adana hukunci a karar da gwamnatin tarayya ta shigar akan gwamnonin jihohin kasar 36 inda ta nemi samun cikakken ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomin kasar 774.

Mai Shari’a Garba Lawal ya shaidawa bangarorin dake cikin shari’ar cewar za’a sanardasu da zarar hukuncin ya kammala.

Mai Shari’ar ya sanarda da batun adana hukuncin ne bayan da kwamitin alkalai 7 na kotun kolin ya karbi kundin bayanan shari’ar daga babban lauyan gwamnatin tarayya kuma Antoni Janar na Tarayya, Lateef Fagbemi, a madadin gwamnatin tarayyar da kuma na gwamnonin jihohin najeriya 36.

A yayin zaman kotun na yau Alhamis, Antoni Janar din ya bukaci kotun data amince da ilahirin bukatun gwamnatin tarayya a karar.

Saidai gwamnonin, ta hannun kwamishinonin shari’arsu, sun kalubalanci bukatun gwamnatin tarayya tare da bukatar kotun tayi watsi dasu.

Fagbemi ya maka gwamnonin a kotu, a madadin gwamnatin tarayyar, inda ya bukaci baiwa kananan hukumomi cikakken ‘yancin cin gashin kai, a matsayinsu na matakin gwamnati na 3 a kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG