Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sansanin Soji A Jihar Neja


Yan bindiga
Yan bindiga

Lamarin ya faru ne a yayin wani artabu tsakanin sojoji da ‘yan bindiga.

Akalla sojoji biyu sun jikkata yayin wani hari da ‘yan ta’adda suka kai sansanin sojoji da ke Tegina, a karamar hukumar Rafi ta Jihar Neja.

Rahotanni daga kafafen yada labaran cikin gida na cewa ‘yan bindigar na kokarin tsallakawa zuwa wasu kananan hukumomin jihar ne, yayin da suka kai harin.

An kuma kashe wani shugaban ‘yan bindiga a harin da ya faru da sanyin safiyar jiya Talata, 11 ga watan Yunin da muke ciki.

A cewar rahotanni, ‘yan bindigar na kan tsallakawa zuwa kananan hukumomin Mashegu da Wushishi na jihar ne da niyan yin awon gaba da shanaye a yankunan a lokacin da suka ci karo da sojoji.

Shugaban karamar hukumar Rafi, Ayuba Katako, ya ce sojoji biyun da aka harbe suna karbar magani a asibitin kwararru na IBB Minna, an kuma kashe daya daga cikin ‘yan fashin da ake zargin shugabansu ne.

Katako ya ci gaba da bayyana cewa sojoji da ‘yan sanda da ‘yan banga suna bakin kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar kuma sun cancanci a yaba musu, inda ya yi fatali da hare-haren da ake ci gaba da kai wa jami'an tsaro.

Ya kuma yi kira da a yi hakuri a bada goyon baya da addu’o’i domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar jihar da ma Najeriya baki daya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG