A yau Alhamis, harkokin zirga- zirgar jiragen sama a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sun tsaya cik yayin da mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka kaddamar da zanga-zangar tare da rufe kofar shiga filin jirgin.
Mambobin kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC da TUC sun tsayar da ayyuka a filin tashi da saukan jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja don nunawa gwamnati bacin ransu a game da zalincin da aka yiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.
Rundunar sojin Najeriya dake aikin samar da tsaro a jihar Filato, wato 'Operation Safe Haven', ta damke daya daga cikin wadanda ake zargi da kisan Ardon yankin Panyam a karamar hukumar Mangu, Alhaji Adamu Idris Gabdo.
A wani muhimmin mataki da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yanke yau Laraba a Maitama, Kotun ta bayar da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele bayan shafe watanni biyar da kwanaki a tsare.
Majalisar Dattawan Najeriya ta yi wani zama na musamman kan rikicin Isra'ila da Falesdinu, inda ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki matakin gaggawa wajen kawo karshen rikicin.
Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta ce ta na shirin tafiya kotu idan har gwamnatin Najeriya ta ki ba ta kaso 13 na kudaden da ake samu daga tashoshin samar da hasken lantarki dake jihar.
Hukumar bada agajin gaggawa ta birnin Tarayya wato- FEMA ta ce fashewar wata tankar Gas ne ta janyo gobarar da ta haddasa mutuwar mutane biyu 'yan Najeriya da kuma raunata wasu karin biyu a fishin jakadancinta da ke Abuja, babban birnin Najeriya.
Ofishin jakadancin kasar Canada ya dakatar da ayyukansa na wani dan lokaci biyo bayan gobarar da ta kama ofishin da yayi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkata wasu.
An doke matashiya ‘yar Nijeriya, Hilda Bassey Effiong da aka fi sani da Hilda Baci, da ta zama sarauniyar dafa abinci ta duniya bayan da ta shiga gasar dafa abinci mafi tsawo wacce ta shafe kusan awa 100 tana dafe-dafen abinci kala-kala.
Wasu ‘yan bindiga sun kashe daliban makarantar Islamiyya 13 a yayin da suke bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da kisan mutane biyar tare da kona kayan abinci da abubuwan hawa, a wani hari da 'yan bindiga suka kai da safiyar Litinin a garin Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto da ke Arewa maso yammacin Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar Labour a zaben shugaban kasa na shekarar 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa hukuncin da kotun kolin Najeriya ta yanke bai karya masa gwiwa ba a kan ganin an sami sauyi a sabuwar Najeriya.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.