Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yayi martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, tare da yin kakkausar suka dangane da tasirin hukuncin da kotun ta yanke a zaben 2023.
Yayin da Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa suka kai ziyarar aiki Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sauya Najeriya daga kasa mai rarrafe izuwa kasa mai dimbin ci gaba.
A kalla mutane sama da 40 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin kwale-kwale da ke dauke da mutane akalla 200 da ya nutse a kogin Billari a karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.
Kungiyar da ke sasanta tsakanin addinai reshen jihar Filato ta ja hankalin majalisar shari’a ta kasa, a kan ta maida hankali wajen yin nazarin yadda kotunan sauraron kararrakin zabe ke gudanar da shari’u, da a ganinsu ke cike da kurakurai, don kaucewa tashin hankali.
A cewar sanarwar da PDP ta fitar a ranar Asabar, Atiku zai yi magana ne a taron manema labarai da zai yi a Abuja ranar Litinin.
“A gaskiya wadannan maganganu da suka fita daga bakin mawakin ya sa na ga cewa tsayawa a ba shi amsa a matakin hankali ma bata lokaci ne." In ji Ahmad.
Kawo yanzu kotun daukaka kararrakin zabe a jihohin kasar ta kori yan Majalisar dattawa 7 da na wakilai 26, kuma har yanzu ba a gama ba tukunna.
Hukumar raya Babban Birnin Tarayya na Abuja ta ce sam ba kamshin gaskiya a labarin da aka yi ta yayata a kafafen sada zumunta cewa Ministan birnin Nyesom Wike zai rushe wani sashen babban Masallacin tarayya da ke Abuja.
Kungiyoyin dai na zargin wasu shugabannin kasashen yammacin Afirka da jefa al'umar Nijar cikin kangin wahalhalu sanadiyyar takunkuman da aka kakaba mata.
Kotun kolin Najeriya mai alkalai 7 karkashin jagorancin mai shari’a John Nyang Okoro, ta yi watsi da kararrakin da Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Leba suka daukaka kan nasarar da Bola Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.
Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da bukatar da dan takarar shugaban kasa karkashin Inuwar Jam’iyyar PDP yayi na gabatar da sabbin hujojji a gaban ta.
Wani batu da ya ja hankalin 'yan Najeriya a kwanannan shi ne na wata daliba da aka kora daga makarantar nazarin kimiyar ayukkan jinya da ungozoma ta jihar Kebbi, da sunan cewa tana badala a dandalin sada zumunta na yanar gizo na Tiktok.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.