Wadansu 'yan aware masu amfani da harshen Ingilishi dauke da makamai sun kai hari wani kauye a kasar Kamaru da yammacin ranar Laraba, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.
Kotun daukaka kararrakin zabe dake zama a Abuja ta warware sakar da kotun sauraren kararrakin zabe a jahar Nasarawa tayi, inda ta ayyana gwamna mai ci, Abdullahi Sule a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna a jahar.
Hukumar alhazan Najeriya NAHCON ta nanata umurnin ajiye Naira miliyan 4.5 daga duk mai niyyar gudanar da aikin Hajjin 2024 gabanin karshen watan gobe.
Wata babbar mota dauke da kayan abinci da mutane sama da 200 ta yi hatsari a jihar Neja da ke Arewa maso tsakiyar Najeriya, inda ta kashe fasinjoji 25 tare da raunata wasu da dama, kamar yadda hukumomi suka bayyana a ranar Laraba.
Majalisar Dattawan Najeriya ta umurci kwamitin ta da ke kula da harkokin shari'a, da yancin ‘dan Adam da na dokoki, da ya yi magana da ofishin Atoni Janar na kasa domin gudanar da bitar dokokin kasar tun daga shekara 2004 zuwa 2023, wadanda aka riga aka rattaba ma hannu domin a sa su a kundi guda.
Kotun Daukaka Kara ta sake jaddada nasarar Gawuna bayan yaduwar wata jita jita.
Fitar da wani sashi na daftarin hukuncin kotun daukaka kara ta Najeriya dake Abuja, dangane da shari’ar zaben gwamnan Kano ya sake dumama yanayin siyasar jihar, dai dai lokacin da masana dokoki da shari’a da kuma manzarta a fagen dimokaradiyya ke bayyana albarkacin bakin su.
Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi watsi da jiya-jitar cewa babban hafsan Hafsoshin tsaron kasar, Janar CG MUSA ya mutu.
Wasu lauyoyi masu da'awar kishin al'ummar Nijar sun shigar da kara kotun ECOWAS a Abuja don bukatar haramta takunkumi kan talakawan Nijar.
Adamawa SP, Sulaiman Yahya Nguroje, kakakin rundunar 'yan sandan jahar, ya tabbatar da faruwar lamarin wa Muryar Amurka amma bai bayyana takamammen abun da ya faru ba.
Yayin da ma'aunin tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 27.33% bisa rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya, masana sun ba da shawarar komawa kan kananan sana'o'i don samun mafita.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.