NARRATION A yayin da al-umomin yankin Birnin Gwari ke kokawa game da hauhawar hare-haren 'Yan-Bindigan da ke hana manoma dibar amfanin gona, gwamnatin Kaduna ta sanar da harbe wasu 'yan-bindiga 6 da kuma kwato makamai da dama a yankunan Birnin Gwari, Giwa da Igabi.
Bayan sanar da hukuncin kotun daukaka kara dake Abuja game da zaben gwamnan Kano wadda ta tabbatar da nasara ga dantakarar Jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna, masana kimiyyar siyasa dana dokokin kasa na ci gaba da fashin baki akan batun.
Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar da dan takarar APC Abubakar ya shigar wacce ke kalubalantar nasarar gwamnan na Bauchi.
Gwamnatin jihar Kano ta jam’iyyar NNPP ta ce za ta je kotun koli, bayan da kotun daukaka kara da ke Abuja ta ce dan takarar jam’iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara a zaben gwamnan Kano daya gabata, kamar yadda kotun sauraren kararrakin zabe ta Kano ta yanke hukunci a kwanakin baya.
Kotun daukaka kara da ke zama a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta soke zaben gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP.
"Duk wanda aka samu da laifin ta da tarzoma a lokacin hukuncin ko bayan hukuncin da kotun daukaka karar za ta yanke zai fuskanci fushin hukuma," kamar yadda wani sashe na yarjejeniyar ya nuna.
Uwargidan shugaban Najeriya Sanata Remi Tinubu ta tallafa wa matan sojojin da suka rasa mazajensu a filin daga da kuma marayun da aka bar masu da kudade.
Kotun daukaka kara ta birnin Yamai a Jamhuriyar Nijar ta fara zaman shari’ar da ke tsakanin gwamnatin kasar da Janar Salou Souleyman wanda aka garkame a gidan yari a watan Disamban 2015 tare da wasu hafsoshin soja da fararen hula a bisa zargin yunkurin juyin mulki, zargin da suka sha musantawa.
Shugabancin kungiyar kwadago ta dakatar da yajin aikin da ake yi a duk fadin kasar, bayan tattaunawar da suka yi da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, malam nuhu ribado.
Babban Bankin Najeriya ya shelanta cewa a ci gaba da amfani da tsoffin kuɗaɗe, kuma babu ranar dakatar da amfani da su, kafin wannan sanarwar, ƴan ƙasar sun fara fuskantar ƙarancin takardun kuɗaɗe a hannuwansu.
Hukumomin mulkin sojan jamhuriyar Nijer sun taya takwarorin aikinsu na Mali murnar samun nasarar sake kwato garin Kidal daga hannun ‘yan tawayen arewacin kasar.
A wani mataki na habbaka harkokin ilimi a Najeriya, gwamnatin kasar ta bada tallafin karatu wa dalibai 179 don zuwa kasar Rasha karo Ilimi, matakin ya biyo bayan shirin karkashin yarjejeniyar ilimi tsakanin kasashen.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.