Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyar A Sokoto


Wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Arewacin Najeriya
Wani hari da ‘yan bindiga suka kai a Arewacin Najeriya

Rundunar  'yan sandan Najeriya ta tabbatar da kisan mutane biyar tare da kona kayan abinci da abubuwan hawa, a wani hari da 'yan bindiga suka kai da safiyar Litinin a garin Gidan Buwai da ke karamar hukumar Rabah a jihar Sokoto da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan harin dai na zuwa ne lokacin da mahukunta ke cewa suna daukar matakai na magance ayukkan ta'addanci a Najeriyar.

Har yanzu wasu al'ummomi a Najeriya suna kasa samun yin bacci da idanu biyu rufe saboda rashin tabbas na matsalar 'yan bindiga, duk da yake wasu lokuta jami'an tsaro na samun galaba a kansu.

A Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya da safiyar Litinin jama'ar garin Gidan Buwai sun wayi gari da rashin mutane biyar sanadiyar harin da 'yan bindiga suka kai garin.

Rundunar 'yan sanda ta Najeriya ta tabbatar da lamarin ta bakin kakakin ta a Sokoto ASP Ahmad Rufa'i, wanda ya ce 'yan bindigar sun shiga garin sun kashe mutane biyar, suka kona kayan abinci da babura da motoci, kafin gada baya jami'an tsaro na hadin gwiwa su kai dauki a garin.

‘Dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Abdullahi Alhaji Zakari, ya nuna damuwa a kan faruwar lamarin, wanda ya ce ba ya rasa nasaba da tsare wani jajirtaccen mutumin garin wanda 'yan bindiga ke tsoro kuma shakkun shiga garin saboda shi.

Ita kuwa rundunar 'yan sanda tace ba ta da masaniya a kan cewa wani jajirtaccen mutumin garin na tsare , abin da zai bayar da dama ga barayin su shiga yankin.

Amma dai a cewar kakakin rundunar, ko ma mene ne, za a ji daga baya da yake tana kan tuntunbar shuwagabannin al'ummar yankin.

Ko kafin wannan harin, an kai wani makamancin sa a garin Duhuwa na karamar hukumar Wurno mai makwabtaka da Rabah duk a gabashin Sokoto wanda ya yi sanadin salwantar rayukan mutum shida, da kuma wata hubbasa da mutane suka yi ta halaka wasu mutane da aka gano suna yi wa 'yan bindiga leken asiri a garin Huci na karamar hukumar Gwadabawa.

Masu sharhi a kan lamurran yau da kullum irin Farfesa Bello Badah na ganin kowa na da gudunmuwar da zai bayar wajen samun mafita daga wannan matsalar.

Fatar 'yan Najeriya dai ba zai wuce ganin kawo karshen wadannan matsaloli na rashin tsaro ba a kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

‘Yan Bindiga Sun Halaka Mutum Biyar A Sokoto.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG