Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canada Ta Dakatar Da Ayyukan Ofishin Jakadancinta A Najeriya


Ofishin jakadancin kasar Canada da ke Abuja
Ofishin jakadancin kasar Canada da ke Abuja

Ofishin jakadancin kasar Canada ya dakatar da ayyukansa na wani dan lokaci biyo bayan gobarar da ta kama ofishin da yayi sanadin mutuwar mutum biyu da jikkata wasu.

Haka kuma ofishin ta yi gargadin rage yawan tafiye-tafiye zuwa Najeriya.

Mummunar gobarar ta tashi ne a wani sashe na ofishin jakadancin kasar Canada da ke Abuja a Najeriya, inda tayi sanadiyyar rasa rayukan mutane biyu tare da jikkata wasu. Lamarin wanda ya afku a safiyar litinin. Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe goma da rabi na safe.

Shugaban ayyuka na hukumar kashe gobara a babban birnin tarayyar Najeriya, Sina Abioye yace gobarar ta tashi ne sakamakon fashewar wata tankar man dizal mai dauke da lita 2,000 na man fetur a lokacin da ake kula da gyaran wadansu injinan bada wutar lantarki guda biyu na MIKANO.

GOBARA
GOBARA

Ministar harkokin wajen Canada Melanie Joly ta jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, ta kuma tabbatar da ci gaba da binciken musabbabin fashewar.

"Za mu iya tabbatar da cewa an samu fashewar wani abu a babban hukumar mu da ke Najeriya. Gobarar ta tashi, kuma muna aiki don yin karin haske kan abin da ya haddasa wannan lamarin," in ji Joly a shafinta na (X)

Melanie Joly
Melanie Joly


A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, shugaba Tinubu ya tabbatar wa hukumomin kasar Canada cikakken goyon bayan gwamnatin Najeriya wajen taimakawa jami’an ofishin jakadancin na diflomasiyya da na kananan hukumomin da gobarar ta shafa.

Haka zalika, sanarwa ta mika addu’o’i ga wadanda suka rasu da kuma samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Duk da cewa hukumar ta ofoshin jakadancin ta kasar Canada a Najeriya kauracewa yin tsokaci kai tsaye kan lamarin da ya faru,dai ta yi amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo inda ta sanar da dakatar da ayyukanta na wucin gadi, har sai baba ta gani.

An danganta wannan matakin da ta dauka da tabarbarewar yanayin tsaro da ya addabi Najeriya, tare da hadurran da ke tattare da ta'addanci, da laifuka, da fadace-fadacen kabilanci, da hare-haren ‘yan bindiga da kuma garkuwa da mutane.

Dangane da wannan mummunan lamari, hukumar tayi babban kira musamman ga ‘ya’yanta su yi taka tsantsan tare da kaucewa tafiye-tafiye barkatai zuwa Najeriya, harda babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Tinubu, wanda ya fi mayar da hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasar, har yanzu bai fitar da wasu sabbin dabaru na magance matsalar rashin tsaro da ya addabi kasar ba, da suka hada da tashe tashen hankula a yankin arewa maso gabas da kuma yawaitar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa a yankin arewa maso yamma.

A baya dai Amurka da Britaniya sun yi gargadin cewa, za a kara fuskantar barazana ga manyan otal-otal a cikin biranen Najeriya tare da ba da shawarar hana tafiye-tafiye barkatai zuwa Najeriya.

Duk da cewa kasashen yammacin duniya kan bayar da gargadi game da balaguro zuwa Najeriya, gwamnatin Najeriya ta sha yin watsi da wadannan sanarwa da cewa ba su da inganci. Sai dai abubuwan da suka faru a baya-bayan nan sun nuna matukar bukatar daukar matakan tsaro da kuma taka tsantsan a cikin kasar.

~Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG