Kotun Daukaka Kara ta sake jaddada nasarar Gawuna bayan yaduwar wata jita jita.
Fitar da wani sashi na daftarin hukuncin kotun daukaka kara ta Najeriya dake Abuja, dangane da shari’ar zaben gwamnan Kano ya sake dumama yanayin siyasar jihar, dai dai lokacin da masana dokoki da shari’a da kuma manzarta a fagen dimokaradiyya ke bayyana albarkacin bakin su.
Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi watsi da jiya-jitar cewa babban hafsan Hafsoshin tsaron kasar, Janar CG MUSA ya mutu.
Wasu lauyoyi masu da'awar kishin al'ummar Nijar sun shigar da kara kotun ECOWAS a Abuja don bukatar haramta takunkumi kan talakawan Nijar.
Adamawa SP, Sulaiman Yahya Nguroje, kakakin rundunar 'yan sandan jahar, ya tabbatar da faruwar lamarin wa Muryar Amurka amma bai bayyana takamammen abun da ya faru ba.
Yayin da ma'aunin tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 27.33% bisa rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya, masana sun ba da shawarar komawa kan kananan sana'o'i don samun mafita.
“Idan so samu ne ma, kafin a yi jana’izarsa in sauke masa duk wani nauyi da ke kansa matukar bai fi karfina ba.” Humaira ta ce.
A ranar Talata ake sa ran za a yi jana'izar marigayin a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
An saki dubban fursunoni a fadin Najeriya daga gidan yari a kokarin da ake na magance cunkoso.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi karin haske a kan wani harin kwanton bauna da mayakan Boko Haram su ka kai a kan tawagar motocin Gwamnan Jihar Yobe.
Tsohon hafsan sojin ya rasu ne bayan ‘yar gajeruwar rashin lafiya da sanyin safiyar Lahadi a asibitin sojoji da ke Legas.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.