Magajin garin Newark, New Jersey a Amurka, Ras J. Baraka, ya karrama Kanyeyachukwu Tagbo Okekene a ranar Lahadi da lambar yabo, a yayin bikin zagayowar ranar samun ‘yancin Najeriya karo na 8 a jihar.
Shugaba Tinubu ya fada wa ministoci da sauran hadimansa a wani taro cewa, ya zabe su ne don su taimake shi ya yi nasara a gwamnatinsa, kuma duk wanda ke aiki yadda ya dace kada ya samu wata damuwa.
Hukumomin shari’ar jamhuriyar Nijar sun sanar cewa binciken da suka gudanar ya bada damar gano wasu karin bayanan da ke gaskanta zargin yunkurin tserewar shugaba Mohamed Bazoum da iyalinsa. Sun ce sun kama kudade da dama da wasu tarin kayayaki a fadar ta hambararren shugaban.
Hatsabibin dan bindigar nan da ake kira Dogo Gide ya sha da kyar bayan da sojojin Najeriya suka samu nasarar hallaka wasu manyan 'yan bindiga uku a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rahotanni daga Najeriya na bayanin cewa, babban bankin kasar, wato Central Bank Of Nigeria (CBN), ya rufe bankuna guda 754 da suka hada da manya da matsakaita da kuma bankunan sayen gidaje a fadin kasar, sakamakon matsalolin da bankunan suka shiga.
Al’amura sun tsaya cik a majalisun dokokin jihohi 36 na Najeriya tun bayan da ‘yayan kungiyar ma’aikatan Majalisun suka tsunduma yajin aiki a shekaranjiya Litinin. Sai dai masu sharhi na cewa yajin aikin ba shine mafita ba.
Kotun daukaka kara da ke zama a birnin Tarayya Abuja ta tabbatar da Natasha Akpoti-Uduaghan ta Jam’iyar PDP a matsayin wadda ta lashe zaben Majalisar Dattijai mai wakiltar Kogi ta Tsakiya
Babban bankin Najeriya- CBN, ya fayyace cewa, babu kanshin gaskiya a jita-jitar da ake yadawa cewa, bankin na shirin canza fasalin takardun kudin kasar a shekara ta dubu biyu da ishirin da hudu.
Ya zuwa yanzu hukumomin yankin sun tabbatar da mutuwar mutum 17 yayin da aka ceto mutum 14.
Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, yayi martani ga hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan, tare da yin kakkausar suka dangane da tasirin hukuncin da kotun ta yanke a zaben 2023.
Yayin da Shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Olaf Scholz da tawagarsa suka kai ziyarar aiki Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, a jawabinsa ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sauya Najeriya daga kasa mai rarrafe izuwa kasa mai dimbin ci gaba.
A kalla mutane sama da 40 ne suka rasa rayukansu a wani hadarin kwale-kwale da ke dauke da mutane akalla 200 da ya nutse a kogin Billari a karamar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.