WASHINGTON, D. C. - Motar dai na kan hanyarta ne ta zuwa cibiyar tattalin arzikin Najeriyar lokacin da ta yi hatsari a kauyen Takalafia da ke gundumar Magama, a jihar Neja a ranar Talata, kamar yadda hukumar kiyaye hadurra ta Najeriya ta bayyana.
Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kai mutanen 25 da suka mutu zuwa dakin ajiyar gawa da ke kusa, yayin da wasu fasinjojin ke jinya sakamakon raunukan da suka samu.
Kumar Tsukwam, kwamandan sashen kiyaye hadurra na Najeriya a Neja, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, an yi imanin wasu fasinjojin sun so tafiya da tirelar ne cikin daren ranar Talata, don guje wa hanyoyin da ba su da tsaro da rana.
Daukan kayan da wuce gona da iri yawan gudu nahaifar da hadarurruka a manyan tituna a Najeriya, inda galibi ba a bin ka'idojin zirga-zirgar ababen hawa, inda kuma direbobin da ke kin bin ka'idar sukan kaucewa hukunci.
Hukumomi za su tabbatar da cewa “an gabatar da hukunci mai tsanani ga masu keta dokar hanya” a jihar Neja, in ji Bago.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya jajanta wa wadanda lamarin ya rutsa da su, ya kuma bukaci matafiya da su rika tuka mota a cikin natsuwa, musamman a lokacin da bukukuwan hutu ke kara gabatowa.
"Shugaban kasar ya bayyana lamarin a matsayin wani abin takaici, kuma ya umurci hukumar da ke da alhakin kai daukin gaggawa da ta gaggauta shiga tare da tabbatar da cewa wadanda suka jikkata sun samu kulawar da ta dace," in ji ofishin Tinubu a cikin wata sanarwa.
-AP
Dandalin Mu Tattauna