ABUJA, NIGERIA - Kwararre a fannin zamantakewar ‘dan Adam ya ce Majalisar ta yi sakaci wajen duba da tattara dokokin tun farko shi ya sa aka shiga wannan yanayi da ake ciki.
Majalisar ta bada wannan umurni ne sakamakon wani kudurin gaggawa da Sanata mai wakiltan Jihar Borno ta tsakiya, Kaka Shehu Lawan ya kawo a gabanta.
Kaka ya ce ya lura cewa kimanin shekaru 19 kenan da yin dokokin da suka shafi kasa, wadanda aka rattaba wa hannu, amma kuma ba a hada su wuri guda a kundi daya ba, sai aka bar su a warwatse.
Kaka ya ce hakan ya haifar da rudani a kasa har ake amfani da dokokin daban-daban masu karo da juna. Kaka ya ce ana tallata dokokin a rarrabe daban-daban a titunan kasar, har malaman makarantu a jami'o'i da dalibai har ma da lauyoyi suna amfani da dokokin ne daban-daban wanda hakan bai dace da kasar ba.
Shi kuwa masanin harkokin shari'a da dokokin kasa Barista Mainasara Umar ya yaba da wannan kuduri, tare da cewa hakan ya nuna cewa a cikin yan majalisar na yanzu, akwai masu kishin kasa.
Mainasara ya ce ya kamata a tattara dokokin a kundi day,a inda za a sa masu suna dokar kasa na shekara kaza zuwa shekara kaza, inda yin wannan kundi ko Gazette ko Codification zai bada dama na yin amfani da dokokin bi da bi, saboda a samu saukin amfani da su.
Mainasara ya bada misali da dokar da ta ba dalibai dama na karban bashi wajen inganta ilimin su, inda ya bada shawara cewa rashin yin gazette din ya sa har za a maimaita dokar ba tareda an sani ba. Ya kara da cewa sa idanu kan irin wannan kuduri abu ne mai kyau kwarai da gaske.
Amma ga kwararre a fanin zamantakewar ‘dan Adam kuma malami a jami'ar Abuja, Dr. Farouk Bibi Farouk, yana ganin sakacin Majalisar kasa ne ya kai su ga wannan hali da ya sa ake wancakalar da dokokin ko ina da ko ina.
Bibi ya ce laifin ya shafi Majalisa da bangaren babban mai shari'a na kasa saboda su ne ya kamata su sa ido a dokokin da majalisa ta amince da su, kuma shugabanin kasa su ka sa hannu kan su.
Ya kuma kara da cewa wani abu da ya dauki hankali shi ne cewa a duk lokacin da aka yi zabe ana zubar da kusan kashi 75 cikin 100 ko kashi 80 cikin 100 na ‘yan majalisar, shi ya sa ake samu kurakurai da dama wajen adana dokoki.
Bibi ya ce wasu ba su san muhimmancin dokokin ba domin ba su aiki da su, saboda haka dole ne a yi gyara sosai.
Abin jira a gani shi ne ko harhada wadannan dokoki wuri daya zai taimaka wajen gudanar da shari'a a Najeriya ba tare da kawo rudani ba.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Dandalin Mu Tattauna