Ga wasu wannan matakin yayi, yayin da wadansu ke tambaya me ya sa a can baya aka hana 'yan kasar shigowa da irin wadannan kayayyakin da ake zargin na zuwa hannun 'yan ta'adda.
An dai dade hukumomin kula da binciken kayan da ke shiga da fita daga Jamhuriyar Nijar suna karbe kayayyakin sadarwa na Internet na Starlink, musamman a kan iyakar Nijar da Najeriya, da zargin cewa kayan na zuwa ne hannuwan 'yan ta'adda da ke anfani da su wajen karfafa ayyukan cikin kasar.
Amma yanzu hukumomin kasar sun baiwa kamfanin Starklink damar baje kasuwar su a Nijar, da zimmar bunkasa harkokin yanar gizo ta hanyar samar wa 'yan kasar Internet mai inganci, abin da ya sa a halin yanzu aka baiwa duk masu bukata damar shigowa da kayan na Starlink bayan sun biya kudaden kwastam da na haraji.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da 'yan kasar ke kukan rashin ingancin yanar gizo na kamfanonin salula na kasar, abin da ya sa ayar tambaya ga ko shin kampanin na Starllink zai maye gurbin kamfanonin cikin kasar.
'Yan Nijar dai, na ci gaba da dakon lokacin soma aikin kamfanin na Starlink a kasar domin bambanta shi da na kamfanonin sadarwa da ke aiki a cikin kasar a halin yanzu.
Saurari ciakken rahoto daga Haruna Mamane Bako:
Dandalin Mu Tattauna