A jawabinsa wajen taron, Ministan cikin gida Janar Mohamed Toumba ya ce aikin da kwamitin ya gudanar tamkar tubalin farko ne aka dasa a yunkrin dora kasa kan sabuwar turbar ci gaba. Ya kuma zayyana wasu daga cikin mafi mahimmanci a shawarwarin da idan aka yi aiki da su za a cimma burin da aka sa gaba.
Ya shaidawa Janar Tiani cewa, daga cikin abinda suka tsayar akwai Kundin Tsarin Mulkin rikon kwarya wanda idan aka kaddamar da shi zai kasance dokokin da za a tafiyar da dukkan lamuran kasa.
Sannan sai wasu kudirorin da suka hada da kayyade wa’adin rikon kwarya na shekaru 5 da za a iya sabuntawa sai batun kara wa Janar Tiani girma zuwa Janar mai tauraro 5 wato General d’armee saboda rawar da ya taka a ayyukan sake gina kasa, sannan a karshe batun rusa jam’iyun siyasa da bullo da wani sabon kundin jam’iyun siyasa wanda ke daidai da tsarin rayuwa da al’adun kasar.
Bayan da ya karbi takardun wannan rahoto daga shugaban kwamitin Dr. Mamoudou Harouna Djingarey, Shugaban gwamnatin mulkin soja Janar Abdourahamane Tiani wanda ya nuna gamsuwa da yadda abubuwa suka wakana. ya yi tunatarwa game da mawuyacin halin tsaron da ake ciki a yankin Sahel, sannan ya gargadi ‘yan kasa akan bukatar canza tunani.
Ya ce, "ba kasar da za ta samu ci gaba cikin yanayin rarrabuwar kai, ba kasar da za ta samu ci gaba da akidar bangaranci, ba kasar da za ta samu ci gaba in ba cikin yanayin hadin kai da akidar gina kasa daga daukacin ‘yayanta ba. "Irin wannan tunanin ne na ke bukatar al’ummar Nijar ta runguma sannan ya kamata daga yanzu a fara maida hankali wajen yafewa juna a manta baya."
Tuni ‘yan kasa sun fara maida martani a game da kiraye-kirayen Janar Tiani.
Tsofaffin Shugabanin kasa Issoufou Mahamadou da Mahaman Ousman da Salou Djibo na daga cikin manyan bakin da suka shaida bikin karbar wannan kammalallen rahoto, wanda a nan gaba ne za a san makomar abubuwan da ya kunsa.
Saurari ciakken rahoton daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna