Yayin da jami'an kamfanin dillacin mai ke danganta matsalar da yanayin da ake ciki a Najeriya jama'a na dora alhakin abin da sakacin masu ruwa da tsaki a sha'anin hada-hadar mai.
Kamar sauran gidajen man da aka yi katarin samun mai da hantsin wannan Litinin motoci da babura ne ke kan layi ko ina. Habibu, wani matashin da ya zo kan babur, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa tun ranar Juma’a da ta gabata yake neman mai bai samu ba.
Wasu dai na dauke da galan-galan a hannu wadanda mafi yawancinsu sun bar motoci ko baburansu ne kan titi sanadiyyar rashin mai a tanki yayin da wasu masu aiki da injin na ban ruwa ne a garake.
Haka su ma direbobin jigila sun fara kokawa game da wannan matsala da tuni ta haddasa tsaiko a harakokin sufuri duk kuwa da cewa akwai wadatar man Diesel.
Mamallaka gidajen mai na dora alhakin yanayin da aka shiga a wuyan kamfanin dillancin mai mallakar gwamnatin Nijar wato SONIDEP.
To sai dai da yake bayani a taron manema labarai darektan sashen kasuwanci a kamfanin SONIDEP Alhaji Aboubacar Ma’azou ya alakanta abin da wasu tarin dalilai.
Ya ce wannan matsala abu dake da nasaba da wasu dalilai, na farko sanannen abu ne cewa a da baki dayan yanki kuduncin kasa na amfani ne da man fasa kwabri. To amma matakin janye tallafin mai a Najeriya ya hana shigowar man zuwa Nijar sannan jami’an tsaro sun dage da farautar ‘yan fasa kwabri a ko ina a fadin kasa abinda ke fayyace bukatar zahiri ta cikin gida.
A baya man da SONIDEP ke samu daga matatar SORAZ ya wadatar to amma da yake babu wancan na bayan fage a kasuwanni, bukata ta karu a cikin gida abinda SORAZ ke badawa ba ya wadatar da jama’a.
Haka kuma faduwar darajar Naira ta shafi wannan haraka. Sannan akwai odar man Nijar da ta makalle a Lome sakamakon matsalar sufuri dake kawo tsaiko kafin man ya iso.
Nijar wacce ita kadai ce Allah ya fuwacewa arzikin man fetur a yankin AES kan samar da man ga kawayenta Burkina Faso da Mali akan farashi mai rangwame lamarin da wasu ‘yan kasar ke ganinsa a matsayin daya daga cikin mafarin halin da aka shiga a nan cikin gida yanzu.
Saurari cikakkne rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna