Shugaba Mahama wanda a washegarin shan rantsuwar kama aiki ya nada wakilin musamman mai kula da yankin Sahel, ya kudiri aniyar sasanta wadannan kasashe da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka, ECOWAS ko kuma CEDEAO.
Karfafa hulda a fannin tattalin arziki, dfilomasiya da tsaro a tsakanin Ghana da Nijar na daga cikin makasudin wannan rangadi na shugaba John Dramani, kamar yadda aka bayyana a sanarwar karshen tattaunawar tawagogin kasashen biyu, wacce ministan harkokin wajen Nijar Bakary Yaou Sangare ya gabatar wa manema labarai.
Ya ce a yayin ganawarsu shugabannin kasashen biyu sun yi farin ciki kan kyakkyawar hulda da dangantakar Ghana da Nijar sannan sun jaddada aniyar daukan matakan da za su ba da damar habbaka wannan hulda ta kai matakin da ya zarce yadda ake zato domin jin dadin al’umominsu.
A game da batun tsaro shugabanin biyu sun tattauna kan yanayin tabarbarewar fannin a yankin Sahel da Afirka ta Yamma saboda haka suka jaddada aniyar hada karfi domin yaki da ta’addancin da aka shafe shekaru ana fama da shi a wannan yanki, lamarin da ke haddasa tarnaki wajen zartar da ayyukan ci gaban da gwamnatoci suka sa gaba.
Tawagogin biyu sun yi amanna game da bukatar karfafa hulda a fannin siyasa, tattalin arziki, kimiya da al’adu, sabili ke nan za su maida hankali wajen musaya a wadannan fannoni a karkashin hukumar hadin gwiwa.
Da yake tsokaci kan wannan ziyar ta shugaban Ghana a kasashen Sahel, kwararre kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye, ya ce Ghana dai har yanzu babu ta’addaci, amma da yake tana makwabtaka da kasashen Burkina Faso da Togo ta wajen arewaci shi ya sa take daukar mataki.
Ko da yake ba a bayyana a fili karara a karshen wannan ziyara ta birnin Yamai ba a sanarwar karshen ganawa da takwaransa na Mali a yammacin ranar Asabar, shugaba Mahama ya sanar cewa ya je ne da niyar sasanta rikicin da ya yi sanadin ficewar kasashen AES daga kungiyar ECOWAS.
John Dramani na ganin a tafi tare ita ce hanya mafi a’ala ga kasashen Yammacin Afirka.
A farkon makon da ya gabata ne shugaban kasar Ghana a yayin ziyara da ta kai shi Cote d’ivoire ya bayyana wa takwaransa Alassan Ouattara shirin tuntubar kasashen AES, don ganin sun koma kungiyar kasashen Yammacin Afirka, kudirin da shugaban na Cote d’ivoire ya yi na’am da shi.
John Dramani wanda tun a washegarin kama aiki ya nada manzon musamman mai kula da yankin Sahel zai kammala wannan rangadi da Burkina Faso a ranar Litinin 10 ga watan Maris.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna