Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Daga Cikin Muhimman Batutuwan Da Trump Ya Tabo A Jawabinsa


Shugaban Amurka, Donald Trump yayin da yake gabatar da jawabinsa
Shugaban Amurka, Donald Trump yayin da yake gabatar da jawabinsa

Trump ya fara jawabinsa ne da cewa "Amurka ta dawo," lamarin da ya haddasa tafi da ihun yabo na "USA! USA!" daga 'yan majalisar jam’iyyar Republican.

Shugaban Amurka Donald Trump, a cikin jawabin da ya yi wa hadakar majalisar dokoki a daren Talata, ya kare sabon harajin kasuwanci da ya kakabawa abokan kasuwancin Amurka tare da yin alkawarin cewa wasu karin haraji na tafe.

“Sauran kasashe sun dade suna amfani da haraji a kanmu, yanzu kuma lokaci ya yi da za mu mayar da martani,” in ji Trump a cikin jawabinsa na farko ga ‘yan majalisar dokoki tun bayan sake darewa kan mulki a wa’adinsa na biyu.

Kalaman Trump sun zo ne bayan da Amurka ta sanya harajin kashi 25% kan kayayyakin da ake shigo da su daga manyan abokan kasuwancinta guda biyu, Canada da Mexico, tare da ninka tsohon harajin kashi 10% da aka sanyawa kayayyakin kasar Sin zuwa 20%. Kasar Sin ita ce ta uku a jerin manyan abokan kasuwancin Amurka.

'Yan majalisar dokokin Amurka suna tafi a lokacin da Trump yake jawabi
'Yan majalisar dokokin Amurka suna tafi a lokacin da Trump yake jawabi

Kasuwannin hada-hadar hannayen jari na Amurka sun fuskanci faduwa mai tsanani, kuma kasashen uku sun yi barazanar mayar da martani, lamarin da ke tayar da hankula kan yiyuwar barkewar yaki na kasuwanci.

Trump ya kuma bayyana cewa Amurka za ta fara sanya “harajin martani” kan dukkan abokan kasuwancinta daga ranar 2 ga Afrilu.

“Duk abin da suka sanya mana haraji a kai, za mu sanya musu haraji a kai. Duk abin da suka karba daga gare mu a haraji, za mu karba daga gare su.”

Ya kara da cewa, “Na so in sa ranar 1 ga Afrilu, amma ban so a ce na yi wasan April Fool ba” na zolaya.

Bugu da kari, Trump ya bayyana shirin sanya harajin kashi 25% kan shigo da aluminum, tagulla, itace, da karfe daga kasashen waje.

Uwargidan Shugaban kasar Amurka, Melania Trump, (dama)
Uwargidan Shugaban kasar Amurka, Melania Trump, (dama)

Jawabin Trump ya zo ne bayan makonni shida da sake karbar mulki, wa’adin da aka fi saninsa da takaddama da kawayen Amurka, sauye-sauyen manufofin kasashen waje, da gyara tsarin gwamnatin tarayya. A ranar Litinin, Fadar White House ta bayyana cewa taken jawabin shi ne "Sabunta Mafarkin Amurka."

Tare da Mataimakin Shugaban Kasa JD Vance da Shugaban Majalisar Wakilai ta Amurka Mike Johnson wadanada suka zauna a bayansa, Trump ya fara jawabin da cewa "Amurka ta dawo," lamarin da ya haddasa ihun "USA! USA!" daga 'yan majalisar jam’iyyar Republican.

Shugaba Trump yana gaisawa da Kakakin Majalisar Wakilai, MikeJohnson.
Shugaba Trump yana gaisawa da Kakakin Majalisar Wakilai, MikeJohnson.

“A makonni shida da suka gabata, na tsaya karkashin rufin wannan majalisa kuma na bayyana zuwan Sabon Zamani Mai Albarka ga Amurka. Tun daga wannan lokacin, ba komai muka yi ba sai daukar matakai cikin gaggawa da azama don shigar da Amurka cikin mafi girma da nasarar zamani a tarihin kasar nan,” in ji shi.

Trump ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa “ta cimma fiye da yawancin gwamnatoci a cikin kwanaki 43 fiye da abin da suka cimma a shekaru hudu ko takwas.”

A halin yanzu, Trump ya rattaba hannu kan kusan umarnin zartarwa 80 — da dama daga cikinsu ana kalubalantarsu a kotu.

Sanata Elissa Slotkin da ta mayar da martanin 'yan Democrat ta ce Amurka na bukatar sauye-sauye masu kishin kasa kuma ya kamata ta kasance jagora mai himma a cikin duniyar da ke da alaka da juna.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG