Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Yankin Sahel Sanadiyar Ta'addanci Ya Karu A 2024 - Bincike


Kungiyar UN - Yaki da ‘yan ta’adda
Kungiyar UN - Yaki da ‘yan ta’adda

Wani rahoton cibiyar nazari da bincike ta Institute for Economics and Peace ya ayyana kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso a matsayin yankin Sahel da ya fi ko ina fama da ta'addanci a duniya a shekarar 2024

Rahoton ya ce daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a bara sanadiyar wannan al'amari, fiye da rabinsu a wadannan kasashen ne abin ya wakana.

Sai dai an fara mahawara kan wadannan alkalumma da wasu ke cewa ba su gamsu da sahihancinsu ba a bisa la'akari da nasarorin da dakarun tsaro ke samu a yankin na Sahel tun bayan sauye-sauyen gwamnatoci da aka fuskanta.

A wannan rahoto da ta fitar a jiya Laraba 5 ga watan Maris 2025 cibiyar mai ofishi a Australia ta ce binciken da ta saba gudanarwa a kowace shekara a kasashe 163 game da yawan hare-hare da illlolin da abin ya haddasaa wannan karo ya gano Mali, Nijar da Burkina Faso a jerin kasashe 5 mafi fama da wannan matsala a duniya a bara inda aka yi asarar rayukan mutane 3,885 daga cikin 7555 da ‘yan ta’adda suka hallaka a duniya.

Abinda cibiyar ta ce ya zarta wanda aka gani a baya.

Cibiyar ta ce Burkina Faso wacce ta fi sauran makwabta yawan mutanen da suka rasu sanadiyar ayyukan ‘yan ta’adda abin ya ‘dan ja baya a wannan karon yayinda Mali ke bi mata sai Nijar wacce duk karancin yawan mutanen da suka mutu adadinsu ya karu idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata, a cewar wannan rahoto.

Sai dai mai sharhi kan sha’anin tsaro AbdoulRahamanAlkassoum na cewa bai gamsu da sahihancin wadannan alkalumma ba.

Rahoton ya kuma kara da cewa yadda matsalolin tsaro ke kara ta’azzara a wadannan kasashe daga shekarar 2017 kawo yanzu musamman a ‘yan shekarun nan 2 na baya alamu ne da ke nunin kaurar ta’addanci daga yankin Gabas ta tsakiya zuwa yankin Sahel.

Shugaban kungiyar MOJEN Siradji Issa na danganta wannan al’amarin da wasu dalilai ne.

To amma kwararre kan harakokin tsaro Amadou Bounty Diallo na alakanta yanayin da aka shiga da tsamin dangantaka da ta taso ne a tsakanin kasashen nan 3 da wasu kawayensu musamman masu manufofin da ya kira na ‘yan mulkin mallaka tun bayan sauye-sauyen mulkin da aka fuskanta.

Cibiyar ta Institute for Economics and Peace a wannan rahoto ta kara da cewa kungiyoyin da suka hada da JNIM ko GSIM da IS a yankin Sahel masu alaka da kungiyar Al-Qaida ne ke da alhakin galibin hare-haren da aka kai a yankin na Sahel a shekarar da ta gabata.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Mutanen Da Suka Mutu A Yankin Sahel Sanadiyar Ta'addanci Ya Karu A 2024 - Bincike.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG