Shirin fim mai taken “No Other Land,” labarin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da ke fafutukar kare al’ummomin su daga yunkurin rushe su da sojoji Isira’ila ke yi, ya lashe kyautar Oscar ta fitaccen shiri na musamman a ranar Lahadi.
A ranar Lahadi, ma’aikatan kashe gobara da ke kokarin kashe wutar daji a jihohin North da South Carolina a Amurka a cikin yanayin bushewar itatuwa da iska mai karfi sun kuma ba da umarni kwashe mutane a wasu yankuna.
Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun musanta a ranar Lahadi cewa an kama wasu mayaka 20 da ke da alaka da kisan kiyashi da aka yi a kasar Rwanda a yankinta, inda suka kira faifan bidiyon na mika su ga Rwanda da cewa “na karya ne.”
Jam’iyyar masu ra’ayin mazan jiya ta Jamus ta lashe zaben kasa da aka gudanar a ranar Lahadi, amma kuri’ar da aka kada ta bai wa jam’iyyar masu ra’ayin rikau ta AfD sakamako mafi kyau a matsayi na biyu.
Jami’ai sun ce sojojin Sudan a ranar Lahadi sun yi nasara a kawo karshen kawanya ta sama da shekara guda a kan muhimmin birnin Obeid, inda suka maido da hanyar shiga wani muhimmin yanki a kudu maso tsakiyar kasar.
Akalla mutum 48 ne suka mutu sakamakon rugujewar wata mahakar zinare da ake aiki ba bisa ka’ida ba a yammacin kasar Mali a ranar Asabar, kamar yadda hukumomi da majiyoyin yankin suka shaida wa kamfanin dillanci labaran Faransa.
Sam Nujoma, dan gwagwarmayar neman ‘yancin kai wanda ya jagoranci Namibia samun ‘yancin kai daga mulkin wariyar launin fata na Afrika ta Kudu a shekarar 1990, ya kuma yi shugaban kasar na tsawon shekaru 15 ya rasu. Yana da shekaru 95.
A cikin wannan shekara da ba ta wuce kwana 40 da kamawa ba, an samu munanan fashewar tankokin man fetur a Najeriya, akalla hudu a fadin kasar, lamarin da ya haifar da mututwar mutane fiye da 200 jumulla, da wasu rahotanni
Shugaba Trump ya yi nuni da cewa za'a sanya wasu karin haraji a makonnin masu zuwa.
Fitacciyar mawakiyar dai ba ta taba lashe kyautar kundin wakoki ba duk da lashe kyautar Grammy 32, fiye da kowane mawaki.
Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta yanke huldar diflomasiyya da Rwanda yayin da ake gwabza fada tsakanin ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda da dakarun gwamnatin a kusa da muhimmin birnin Goma na gabashin kasar.
Domin Kari