Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Jinkirta Matakin Sakawa Canada, Mexico Haraji


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Shirin saka harajin har ila yau ya yi sanadiyyar faduwar farashin hannayen jari na tsawon kwanaki tare da kawo cikas ga dangantakar Amurka da kawayenta da suka dade da kuma manyan abokan cinikiyyarta biyu.

Shugaban Amurka Donald Trump ya jinkirta saka sabon haraji kan yawancin kayayyakin da ake shigowa da su daga kasashen Mexico da Canada zuwa Amurka da tsawon makonni hudu, .

Wannan shi ne matakin da ya dauka na baya bayan nan a sa-in-sa ta fuskar kasuwanci a yankin Arewacin Amurka.

Shirin saka harajin har ila yau ya yi sanadiyyar faduwar farashin hannayen jari na tsawon kwanaki tare da kawo cikas ga dangantakar Amurka da kawayenta da suka dade da kuma manyan abokan cinikiyyarta biyu.

Da farko Shugaba Trump ya jinkintar haraji kan kayayyakin Mexico da ake shigowa da su zuwa Amurka har sai ranar 2 ga watan Afrilu, bayan ji kai-tsaye daga shugabar kasar Mexico Claudia Sheinbaum kan yadda gwamnatinta ta taimaka wajen dakile kwararowar bakin haure da mummunar kwayar fentanyl zuwa Amurka, bukatu biyu da Trump ya nema daga makwabciyar Amurka da ke kudanci.

Sa’o’i bayan haka, ya kuma dakatar da kudin fito kan Canada, ko da yake ba a san abin da zai faru da batun haraji nan da wata guda kan kowace kasa ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG